✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai biya tsoffin sojojin Biyafara kudaden fansho

Minisan Tsaro ya ce za a biya su sauran hakkoki bayan Buhari ya yi musu afuwa.

Gwamnatin Tarayya ta amince a fara biyan tsoffin sojojin Biyafara suka yi yakin basasar neman ballewa daga Najeriya kudaden fansho.

Hukumar Fansho ta Sojoji (MPB) ta ce tsoffin sojojin Biyafara 102 daga cikin wadanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa afuwa ne za su ci gajiyar kudaden fanshon da kuma sauran hakkoki.

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce a halin yanzu mutum 102 din ne za su ci gajiyar kudaden fanshon da sauran hakkoki, saboda yawancin tsoffin sojojin Biyafaran sun riga sun rasu.

Magashi ya kuma bukaci sauran tsoffin sojojin Biyafara da ba a kai ga gano su ba, kuma suke da kwararan dalilai, da su gabatar da kawunansu, domin a tantance su a shigar da su cikin tsarin.

Ya sanar da haka ne a taron ministoci da aka shirya domin kaddamar da bubukuwan Ranar Tunawa da ’Yan Mazan Jiya na 2022, a Abuja ranar Juma’a.

A cewarsa, “Sanin kowa ne cewa tsarin gwamnati mai ci ne yaki da rashawa, don haka Ma’aikatar Tsaro da Hukumar Fansho ta Sojoji suke tantance tsoffin sojoji masu karbar fansho a-kai-a-kai domin dunkule tsarin a wuri daya da kuma toshe duk wata kafa da za a iya amfani da ita wajen aikata almundahana.

“Za mu ci gaba da tattaunawa da tsoffin sojoji ’yan fansho ta hanyoyin da suka dace kamar Kungiyar Tsoffin Sojoji, Sashen Kula da Tsoffin Sojojin da Suka Halarci Yaki da kuma Hukumar Fansho ta Sojoji domin tabbatar da ganin gwamnati na sauke duk hakkokinsu da ke wuyanta.