Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub ya ce gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tana aikin gina tituna kusan guda 26 a iya jihar Kano kawai.
Ya ce tuni aka kammala wasu daga ciki kuma mutane suka fara amfani da su, yayin da kuma ragowar ake sa ran kammala su kafin karewar wa’adin gwamnatin a 2023.
- NBC ta tsawaita wa’adin biyan bashi ga kafofin labaran da ta soke lasisinsu
- Ambaliyar ruwa ta lalata yankuna 225 a Kano da Jigawa
Ministan ya bayyana haka ne a Kano ranar Asabar, lokacin da yake duba aikin mayar da titin Kano zuwa Katsina mai hannu biyu.
Ya ba da tabbacin cewa za a kammala dukkan manya da kananan ayyukan da shugaba Buhari ya fara kafin karewar wa’adin gwamnatinsa.
Ministan ya kuma ce, “Wannan aikin fadada titin Kano zuwa Katsina ya koma mai hannu biyu yana daya daga cikin ayyukan tituna kimanin guda 26, manya da kanana, da Gwamnatin Buhari take yi a Kano.
“Titi ne mai matukar muhimmanci, kuma dan kwangila ya shaida mana cewa yanzu haka matsayin kammala aikin ya kai kimanin kaso 83 cikin 100.
“Sun ba mu tabbacin gamawa kafin karewar wa’adin gwamnatinmu, amma mu ko nan da karshen shekarar nan [2022] aka kammala shi, haka muke so.
“A baya titi ne mai hannu daya, amma a yanzu an mayar da shi hannu biyu, kuma ba wai faci kawai ake yi masa ba, sabunta shi ake sake yi,” inji Umar EL-Yakub.
Ministan ya kuma yaba wa kamfanin CCECC da yake gudanar da aikin wanda ya ce yana iya kokari wajen kyautata aikin, duk kuwa da kalubalen da yake fuskanta.
Sai dai ya hore su da su dada jajircewa wajen ganin aikin ya kammala cikin lokaci.
Shi ma da yake tsokaci a kan aikin, Daraktan Kula da Manyan Hanyoyi na Ma’aikatar, Injiniya Wasiu Tayo, ya ce ba sa ko tantamar yiwuwar kammaluwar aikin a kan lokaci kasancewar an mayar da kwangilar shi cikin shirin SUKUK, don haka ba sai an jira gwamnati ta yi kasafin kudi ba kafin a sami kudin biyan dan kwangila.
Idan za a iya tunawa, tun a shekara ta 2013 ne dai Gwamnatin Tarayya ta bayar da aikin titin na Kano zuwa Katsina, wanda ya fara tun daga shatale-talen garin Dawanau da ke jihar Kano har zuwa garin Katsina.
Bugu da kari, Minista EL-Yakub ya kuma duba wani aikin titin da ya tashi daga kauyen Yakasai ya wuce ta Badume zuwa Damargu ya karasa Marken Zalli da ke karamar hukumar Bichi a jihar ta Kano.
Tuni dai aka kammala tare da fara amfani da akasarin titin mai tsawon kilomita 38.8.