✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi magana kan zaben Gwamnan Edo

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP murnar sake lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, 19…

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP murnar sake lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasar a kan sabuwar hanyar sadarwa, shi ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba.

Shugaban kasar ya ce alwashin da ya sha kan batun gudanar da zabe na gaskiya da adalci na nan daram.

“A tsaye nake kyam wajen ganin an gudanar da zabe na gaskiya da adalci, don ba tare da an gudanar da sahihin zabe ba, tubulin ikonmu na siyasa zai yi rauni.”

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnan wanda ya samu kuri’u 307,955 ya yi nasara a zaben bayan da ya tika babban abokin karawarsa da kasa, Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC mai kuri’u 223,619.