✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi ganawar sirri da shugabannin kabilar Igbo

An hana ’yan jarida daukar zaman shugabannin kabilar Igbo da Buhari a Imo

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da shugabannin kabilar Igbo da ke yakin Kudu maso Gabas.

An hana ’yan jarida shiga zauren taron Buharin da Shugabannin na kabilar Igbo a ranar Alhamis, a lokacin da ya ziyarci Jihar Imo.

Mahalarta taron sun hada da Shugaban Uwar Kungiyar Kabilar Igbo ta Ohaneze, Farfesa George Obiozor da sauran kusoshin yankin.

Sauran mahalarta zaman sun hada da Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, da Mataimakin Gwamann Jihar Abiya, Ude Okechukwu.

Shi ma Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema, da Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje, Cif Uche Ogar, na daga cikin wadanda suka halarci zaman.

Babu bayanin abin da aka tattauna a zaman, amma dai an jima ana ta maganganu kan ba wa yankin Kudu damar fito da Shugaban Kasa a zaben shekarar 2023.

Kawo yanzu dai babu tabbacin yankin da manyan jam’iyyun siyasan Najeriya za su fitar ta ’yan takarar shugaban kasarsu a tsakanin yankin Kudu maso Yamma (yankin Yarabawa) da Kudu maso Gabas (Yankin Igbo) ko Kudu maso Kudu (wadanda su ne marasa rinjaye, masu kananan kabilu).

Hasali ma babu tabbacin daga ina ’yan takarar za su fito, tsakanin yankin Arewa da yankin Kudu; Batun mulkin karba, ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ko na jami’yyun siyasa — tsari ne kawai na fahimtar juna.

Baya ga batun takarar shugaban kasa, akwai masu karajin neman ballewa daga Najeriya a yankin, masu goyon bayan haramtacciyar kungiyar IPOB, wadda ake zargin na samun goyon bayan wasu manyan yankin.

Buhari ya ziyarci Jihar Imo ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar Hope Uzodinma ya kammala.

A lokacin ziyarar tasa jihar Imo, wadda hare-haren IPOB suka yi  wa sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi —har da na jami’an tsaro da hukumomin gwamnati — Shugaban Kasar ya yi alkawarin taimaka wa gwamantin jihar wajen magance matsalolin tsaro da suka yi mata katutu,