✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi ganawar sirri da Buratai

Ganawar sirrin na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun kashe sojoji 16, cikinsu har da hafsoshi a jihar Katsina.

Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari yana ganawar sirri da Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai.

Ganawar tasu na zuwa ne bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji 16, cikinsu har da hafsoshi, a wani kwanton bauna da suka yi wa sojojin a jihar Katsina.

‘Yan bindigar sun kuma raunata sojoji 30 a harin na kauyen shimfida da ke Karamar Hukumar Jibia.

Kwanaki kdan kafin nan wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida cikinsu har da jami’ar ‘yan sanda a jihar Kaduna mai makwabtaka da jihar Katsina, mahaifar Shugaba Buhari.

Skakmakon hare-haren ‘yan bindiga a jihar Katsina, a ranar 18 ga watan Yuni Shugaba Buhari ya bayyana bacin rai kan abin da ya kira gazawar manyan hafsoshin tsaron Najeriya wajen magance matsalar tsaro a kasar.

Ma ba shi shawara kan tsaro, Babagana Monguno ya ce, shugaban ya fada musu cewa ya gaji da yi musu uzuri, don haka su san na yi.

Bayan sun fito daga wancan taron ne Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya bayana wa manema labarai cewar Shugaban kasa ya damu matuka kan tabarbarewar tsaro a kasa.

Monguno ya ce, Buhari ya gaya musu cewar an zabe su ne domin ya samar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma farfado da tattalin arzikin kasa. Kuma aikin ba zai gudana ba sai an samu cikakken tsaro.

Ya kuma ce Shugaban kasa ya ce ba za’a samu nasarar kawo karshen rashin tsaro a kasar nan ba sai an magance sayar da layukan waya da aka riga yi wa rajista.

Shugaban Kasa ya kuma umarce su da su yi aiki tare da Ministan Sadarwa, Isa Pantami domin shawo kan matsalar.

Ya kuma nemi su hada kai da Shugaban ‘Yan Sanda da Shugaban Hukumar tsaro ta DSS wajen dakile sayar da layukan waya da ka riga aka yi wa rajista.