Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu, murnar cika shekara 50 tare da yi masa addu’ar samun karin lafiya da basira.
Sakon taya murnar da Buhari ya aike ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, ta jinjina wa sarkin bisa kokarinsa wajen wayar da kan al’ummar masarautarsa game da abin da ya shafi rayuwarsu musamman a lokcin annobar COVID-19.
- ‘Abin da ya kamata ka yi a matsayinka na Sarkin Zazzau’ —El-Rufai
- Kasafin 2021: Noma da Arewa maso Gabas na bukatar kudade —Monguno
- Kotu ta soke daukar ’yan sanda 10,000 da aka yi a 2019
Buhari ya ce sarkin ya zama abin koyi wajen taimakon jama’a da kuma wanzar da hadin kai da hukuri da zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Shugaban kasar ya ce kokarin sarkin karfafa wa matasa gwiwar rungumar neman ilimi da sana’o’in dogaro da kai abin yabawa ne.
Ya kuma taya iyalai da masoya a da abonkan sarkin da ma daukacin jama’ar Masarautar Bauchi murnar cikar Sarkin shekara 50 a duniya.