✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya saki kudi kawai talaka ya ji dadi —Tinubu

Buhari rika sakin aljihun gwamnati ta yadda kudade za su kai ga talakawa

Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce jazaman ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rika sakin aljihun gwamnati ta yadda kudade za su kai ga talakawa.

Tinubu, yayin jawabi a taron cikarsa shekara 69, ya bukaci Buhari ya dain matse bakin aljihun gwamnati, ya rage talauci a tsakanin ’yan Najeriya.

Ya jaddada muhimmancin aiki tare tsakakin bangaren zartarwa da Majalisar Tarayya wajen samar da kudi domin saukaka wa ’yan Najeriya yanayin rayuwar da kasar ke ciki.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas din ya ce, ya kamata Najeriya ta yi wa tsare-tsarenta na tattalin arziki gyaran fuska.

“Yanzu lokaci ne na bayar da muhimmanci ga tsare-tsaren tallafi, ba lokacin tsuke bakin aljihun gwamnati ko takure tattalin arziki ba, a’a lokaci ne na samar da karin dama,” inji shi, a lokacin da yake jawabi.

Da yake buga misali da shirin tallafin da gwamnatin Amurka ta yi a baya-bayan nan, Sanata Tinubu ya bayyana damuwa game da karuwar rashin aikin yi tsakanin ’yan Najeriya a zamanin gwamnati mai ci.

“Kashin aikin yi ya karu zuwa kashi 33%, amma kuna cewa mu yi ta azami; Wanda muke yi ma na nafila ne kuma shafe shekaru muna yi.

“Allah Ya sa Majalisar Tarayya da Shugaban Kasa ba za su rika tsuke aljihun gwamnati ba,” a cewar Sanata Tinubu.

Ya ce, jihohi ne za su iya matse aljihunsu don samun damar aiwatar da kasafin kudinsu amma ba Gwamnatin Garayya ba.

Gwamnatin Tarayya a cewarsa, ita ke da cikakken iko a Najeriya, saboda haka ita ce za ta yi amfani da ikon nata wajen inganta rayuwar al’ummar kasar.