✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nemi yafiyar ’yan Najeriya

Kwana 38 kafin saukarsa daga mulki, Buhari ya gode wa ’yan Najeriya bisa yadda suka yi ta hakuri da mulkinsa ma tsawon shekaru takwas.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki duk ’yan Najeriya da ya yi wa ba daidai ba a lokacin mulkinsa su yafe masa.

Buhari ya kuma bayyana godiyarsa ga ’yan Najeriya bisa yadda suka yi ta hakuri da mulkinsa ma tsawon shekaru takwas.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ’yan kasar mazauna Abuja da suka kai masa ziyarar gaisuwar Karamar Sallah a ranar Juma’a a Abuja.

Buhari ya karbi bakuncin nasu ne a Fadar Shugaban Kasa bayan da ya halarci Sallar Idi a Filin Idin Barikin Soji na Mambilla da ke Abuja.

Hakan kuwa na zuwa ne kwana 38 kafin ya ga shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.