Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro Hukumar Kare Bayanai ta Kasa (NDPB), tare da nada shugabanta.
- 2023: Zawarcin da APC ke wa Kwankwaso ya tayar da kura
- Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC
Shugaban Kasar ya kuma amince da bukatar Farfesa Pantami ta nada Dokta Vincent Olatunji daga Jihar Ekiti a matsayin Kwamishina na Kasa kuma Shugaban NDPB nan take.
Kafin sabon mukaminsa, Doka Vincent shi ne Daraktan Gudanarwa ta Intanet a Hukumar Bunkasa Fasahar Zamani ta Kasa (NITDA)
Kakakin Ministan, Uwa Suleiman, ta ce, “NDPB za ta dora a kan nasarorin da aka samu a karkashin dokar tabbatar da kare bayanai ta kasa, sannan ta taimaka wajen samar da muhimman dokokin kare bayanai.”
Ta bayyana cewa ayyukan sabuwar hukumar sun hada da kare bayanai da kuma hana yi musu kutse da dai sauransu, wanda ya zo daidai da abin da kasashen da suka ci gaba suke yi.