✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya kafa kwamitin samarwa da raba man fetur a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin mutum 14 da zai kula da samarwa da rarraba albarkatun man fetur, da kuma lalubo hanyoyin…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin mutum 14 da zai kula da samarwa da rarraba albarkatun man fetur, da kuma lalubo hanyoyin magance matsalolin da fannin ke fama da su.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Shugaba Buharin a matsayinsa na Ministan Mai, sai Minista a Ma’aikatar Man, Temipre Sylva da zai zama Mataimakin Shugaba.

Cikin wata sanarwa da hadimin Shugaban a bangaren yada labarai Horatius Egua ya fitar ranar Talata, ya ce kwamitin zai tabbatar da aiki ba tare da rufa-rufa ba, da kuma tabbatar da man ya wadata a fadin kasar.

Domin tabbatar da hakan, Egua ya ce Sylva ya umarci Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta tabbatar kan farashin da gwamnatin ta amince ake cinikinsa a ko ina a Najeriya.

Ministan ya kuma umarci NMDPRA ta tabbatar ta kare maslahar al’umma a yanke farashin fetur da kananzir da iskar Gas da albakatun man.