Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbbin takardun Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira 1,000 a safiyar Laraba.
Buhari ya kaddamar da takardun kudin ne gabanin fara taron Majalisar Zartawa ta Tarayya da ke gudana a Fadar Shugaban Kasa.
- Hako mai a Kolmani: Gwamnonin Bauchi da Gombe sun amince su yi aiki tare
- DAGA LARABA: Maganin Karfin Maza: Gyara Ko Janyo Ciwo?
Hadiman Shugaban Kasa irinsu Bashir Ahmad, Buhari Sallau da kuma Bayo Omoboyiowo sun ta fitar da hotunan sabbin takardun kudaden ta shafukansu na Twitter.
A ranar 15 ga watan Disamba mai kamawa ne dai sabbin takardun za su fara aiki kafa-da-kafada da wadanda ake amfani da su a halin yanzu.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da ranar 31 ga watan Janairu, 2023 a matsayin ranar daina amfani da takardun Niara 200, 500 da 1,000 da ake amfani da su a halin yanzu.
Tuni dai ta sanar da al’ummar Najeriya tare da bukatar su da su kai kudaden da suke da su zuwa bankuna domin sauyawa da sabbin da Buhari ya kaddamar a ranar Laraba.
CBN ya bayyana cewa a janye tsoffin takardun da amfani da su ne a hankali.
Idan ba a manta ba, batun sauya takardun kudaden dai ya tayar da kura, amma CBN da Shugaba Buhari suka ce babu gudu, babu ja da baya.
Kawo yanzu dai akwai masu kiraye-kiraye, ciki har da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa, da al’ummar makiyaya da ke neman a kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun.