Ministar Agaji da Ayyukan Jinkai, Sadiya Umar Farouk, ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya kai da fata wajen ganin ’yan Najeriya sun fita daga kangin talauci.
Minista Sadiya ta ce a kan haka ne Shugaba Buhari ya umarci ma’aikatarta ta dauki matasa a rukuni na uku na shirin N-Power, wanda miliyoyin matasa za su samu horo a bangaren fasaha da za su taimaka musu wajen samun sana’o’in dogaro da kai daga baya.
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin ‘N-Knowledge’
- Najeriya A Yau: Shin fitar da ’yan Najeriya Kasashen waje aiki zai taimake ta?
Sadiya ta ce kudurin shugaban kasar na fito da miliyoyin ’yan Najeriya daga fatara da rashin aikin yi ne ya sa shi ba da umarnin fadada shirin.
Ta ce a karkashin shirin tallafin kudade na CCT kuma, Gwamnatin Tarayya na raba wa marasa karfi kudade da kowane wanta domin taimaka musu wajen samun bukatunsu na yau da kullum.
A halin yanzu, a cewarta, an fadada shirin na CCT ta yadda mata mazauna dubban yankunan karkara za su ci gajiyar sa.
Gwamnatin Tarayya na tallafa wa masu mananan sana’o’i da kungiyoyio da rance domin gudanar da sana’o’insu a karkashin shirin tallafin kasuwanci na GEEP.
Sadiya ta ce an fadada shirin GEEP ta hanyar bude rassansa a cikin al’ummomi da kananan hukumomi domin ainihin mutanen da suka cancanta su amfana da shirin na tallafin kananan ’yan kasuwa.
Ministar ta bayyana haka ne a taron mika kwanukan cin abinci domin shirin ciyar da daliban firamare a Jihar Kogi.
Ta ce baya ga yara miliyan tara da ake ciyarwa a makarantu, Gwamnatin Tarayya za ta ba jihohi da ke jan ragamar shirin karin kudade, domin a kara dalibai miliyan biyar a kan masu amfana da shirin ciyarwan.
Sadiya ta ce yin haka zai samar wa karin daruruwan mutane ayyukan yi, don haka ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su kara bayar da goyon baya ta hanyoyi daban-daban domin ganin shirin ya kai ga nasara.
Ta ce kudaden da kawai ake bukata daga gare su a kan shirin shi ne na gudanarwa, amma Gwamnatin Tarayya ce za ta ba da kudaden abincin, jigilarsu, gyara su da kuma bayarwa ga dalibai.