✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya biya likitocin COVID-19 biliyan N8.9

An biya likitoci karin alawus na Naira biliyan 8.9 da suke bin gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta biya ma’aikatan lafiya karin Naira biliyan 8.9 a matsayin alawus din yaki da cutar COVID-19.

Shugaba Buhari ya bayar da izimin ne bayan gwamnatin ta cimma matsaya da kungiyar ma’aikatan lafiya kan janye yajin aikin da a baya suka fara.

“Shugaban Kasa ya ba izinin ba da karin biliyan N8.9 na alawus din hadarin wurin aiki ga dukkannin ma’aikatan lafiya.

“Za kuma a ba da muhimmanci ga samar da kayan kariya a asibitoci da cibiyoyin kula da masu cutar”, inji Sakataren Gwamantin Tarayya Boss Mustapha, a jawabinsa ga kwamitin yaki da cutar ta kasa.

Ya shaida wa taron a ranar Alhamis cewa a yayin da ake ta maganganu kan yajin aikin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya, Gwamantin Tarayya ta yi nisa wajen tattaunawa da su domin warware matsalar.

Boss Mustapha ya ce duk da haka yana da kyau a fahimci cewa Najeriya, kamar sauran kasashen duniya na cikin mawuyacin hali sakamakon annobar COVIV-19 da ta shafi bangaronin rayuwa da tattalin arziki da kudaden shiga na gwamnati.

“Yana da muhimmanci ga dukkannin ’yan kasa, komai aikinsu, musamman ma’aikatan lafiya su nuna tausayi da kishin kasa.

“Lafiyar al’umma da cigaban kasarnmu na da muhimmanci saboda haka mu yi watsi da duk wani mataki da zai kawo koma-baya ga nasarar da aka samu kawo yanzu a yaki da cutar”, inji shi.