✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na jagorantar taron Majalisar Zartarwa

Ana zaman ne a makon cikar wa'adin da ya ba ministoci su mika rahoton zamansu da jama'a

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagornatar taron Majalisar Zartarwa ta Kasa na ranar 4 ga Nuwamba, 2020.

Taron na gudana ne a a daidai lokacin da wa’adin mako guda da Buhari ya ba wa ministoci kowannensu ya kawo rahoton ganawarsa da jama’ar jiharsa ke cika.

A zaman Majalisar na makon jiya Buhari ya wa da wa’adin bayan ya lura biyu daga cikinsu ne suka kammala hada rahoton zaman da ya umarci kowannensu ya yi da jama’ar jiharsa domin dakile maimaituwar tashin hankali da aka gani a lokacin zanga-zangar #EndSARS.

Manayn jami’an da suka hallara a zaman sun hada da Sakataren Gwamantin Tarayya, Boss Mustapha; Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da Ministan Bunkasa Wasanni da Harkokin Matasa, Sunday Dare.

A dakaci karin labarin.