Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya halarci daurin auren babban dan Sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da na dan Ministan Noma, Musa Sani Zangon Daura da aka gudanar ranar Juma’a a Sakkwato.
Gwamnonin da suka halarci daurin auren sun hada da na Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamna Muhammed Badaru Abubakar na Jigawa da kuma takwaransa na Neja, Abubakar Musa Bello.
- Hukumar NBC ta janye dakatarwar da ta yi wa kafofin labarai
- Ranar Hausa: Dalilin da muka fi mayar da hankali kan addu’o’in zaman lafiya
Shugaba Buhari, wanda Ministan Harkokin ‘Yan sanda, Muhammadu Maigari Dingyadi ya wakilta, shi ne ya yi wa Musa Zangon Daura waliyyci yayin da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ya waliyyci Yarima Kabiru.
Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru da takwaransa na Neja, Abubakar Bello ne suka wakilci amaren biyu – Aishat da Nabila.
Amaren biyu dai ’ya’yan fitaccen hamshakin dan kasuwar nan ne na Jihar Sakkwato, Alhaji Umarun Kwabo AA.
Sarkin Malaman Sakkwato, Malam Yahya Na-Malam Boyi ne ya daura auren bayan an biya Naira 250,000 a matsayin sadakin kowace amarya.
Sauran malaman da suka albarkaci auren sun hada da: Shugabannin Kungiyar Izala da Qadriyya ta kasa, Sheik Bala Lau da Sheikh Kharibullah Nasiru Kabara da Sheikh Aminu Daurawa da dai sauransu.