Fadar Shugaban Kasa ta karyata ikirarin cewa Shugaba Buhari, ya bukaci gwamnonin jam’iyyar APC su zabo dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a zaben 2023.
Mashawarcin Shugaban Kasa na Musamman kan Yada Labarai, Femi Adesina, ya ce sabanin labaran da ke yawo, ganawa kawai Buhari ya yi da gwamnonin, inda ya bayyana musu “fatansa” a zaben fid-da dan takarar shugaban kasar jam’iyyar da ke tafe.
- Jiragen yaki ba za su iya kawar da ’yan bindiga ba —Farfesa Usman
- Rayuwar guragun Abuja a baca bayan shekara 15 da alkawarin gina musu mazauni
Hadimin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata kasida kan ziyarar da Buhari ya kai kasar Spain domin halartar taro.
Da yake karin haske kan abin da ya faru a ganawar Buhari da gwamnonin, Femi Adesina ya ce, Buhari bai tattauna batun karba-karba ko masalaha da ko dauki-doran dan takara ba da gwamnoni.
A cewarsa, Buhari ya dai shaida musu abubuwan da zai so gani a zaben fid-da dan takarar shugaban kasar APC.
Amma ya ce, “Babu wata magana game da karba-karba ko masalaha ko dauki doran dan takara.
“Kawai ya bukace su ne da su hada kai a shirye-shiryensu, domin jam’iyyar ta samu nasara; Ana gama taron kuma muka nufi filin jirgin sama.
“Bayan dan lokaci da fara tafiyar tamu ta sa’a biyar, na shiga kafafen sada zumunta, na ga an tayar da yamutsi. Abinka da wasu ’yan Najeriya.
“Idan ba babu takaddama, za su kirkiro, saboda ba za su iya zama shiru ba.
“Damuwarsu kuwai ita ce ya yi amfani da kalmar ‘Magajina,’ maimakon ‘Dan takarar APC.’ Suka ce yana son yin magudin zabe.
“Da kuma ya ce, ya ce gwamnonin da suka yi aiki mai kyau a ba su damar samun wa’adi na biyu, don ci gaba, sai suka ce so yake ya yi dauki dora ko a yi masalaha.
“Da bai yi maganar karba-karba ba kuma suka ce so yake ya ba wa dan Arewa takara.”