✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari a matsayin tatsuniya? (2)

Yaya aka yi wadannan shugabanni, musamman ma Shugaba Buhari suka kasance tamkar tatsuniyar Hausawa ga mabiya da sauran ’yan Najeriya a cikin wannan yanayi da…

Yaya aka yi wadannan shugabanni, musamman ma Shugaba Buhari suka kasance tamkar tatsuniyar Hausawa ga mabiya da sauran ’yan Najeriya a cikin wannan yanayi da muke ciki? Ba za mu gane amsar wannan tambaya ba sai mun fahimci yadda tatsuniyar Hausawan take da yadda take yin tasiri ga rayuwar yara da ake yi wa tatsuniyar ko kuma su ‘talakawan’ da ke bayar da ita.

A tsakanin al’ummar Hausawan dauri, (domin ban sani ba ko har yanzu ana yi, ko kuma tsari da zubin tatsuniyar ta da haka take a yanzu, ko kuma dai an samu makwafin tatsuniyar da wani abu irinta ko wanda ma ya fi ta), ana yin tatsuniya a matsayin makarantar farko a tsakanin al’ummar Hausawa, wadanda kuma suke kan gaba wajen gabatar da ita su ne sababbin amare ko tsofaffin mata da kuma matan aure baki daya. Duk da cewa tatsuniya karya ce ake zubawa amma da yake an gina ruhinta bisa karantarwa da horarwa da zama abin sa nishadi da hani da horo da kuma ma’adanar tarihi da al’adun al’umma, yawancin yara masu sauraren ta ba su dauke ta a matsayin zuki-ta-malle ba, gaskiya ce, shi ya sa ake amincewa da ita, ake kuma yarda da ita, a kuma amince da sakon da ta fito da shi, uwa-uba ana nuna yarda da aminci da duk wani zance da ya fito daga bakin amaryar ko tsohuwar ko kuma mata ko wadansu da ke gabatar da ita.

Mu dauki misalin abin da ke faruwa bayan an kammala tatsuniyar can cikin dare, idan ta kasance mai sa dadi da annashuwa ce, za a ga yara na shewa da dariya kafin su wuce dakunansu domin su kwanta, in kuma ta kasance ta ban tsoro da tashin hankali, wadansu daga cikin yaran ba sa ko iya tunkarar dakunansu saboda tsoro, wadansu kuma sai an goya su ko rike musu hannaye kafin su isa ga makwancinsu. Wannan da kuma yadda wadansu daga cikin yara ke yin sammako zuwa bayan gida ko daki domin jiran kiyashi da ke jan jakar kudi domin su kwashi rabonsu ya kara tabbatar mana da irin amannar da wadansu ke yi wa tatsuniya, duk da cewa karya ce asali ko tushenta.

Bisa irin wannan tunani ne na dora shugabancin Buhari a cikin kusan shekara hudu da yake kan mulkin Najeriya. Bisa irin wannan sikeli ne na auna abin da ke faruwa ga wadansu daga cikin ’yan Najeriya a yau dangane da sake zaben Buhari a karo na biyu a zaben 2019. Me ya sa?

Alhaji Bello Dan Sha Biyu ne ya ja tunanina har na kara amincewa da wannan tunani, domin kamar yadda yake wakewa a bakandamiyarsa ta Motar Siyasa, inda yake cewa ana yin wanka ne da dare saboda fitar da za a yi gobe, ma’ana, ana shuka alheri ne domin a tarbi abin da zai wakana nan gaba, shi wanda ya shuka sharri wa zai sake zabarsa. Ba wai nufina ba ne in ce abin da gwamnatin Buhari ta yi a cikin shekara kusan hudu, ba alheri ba ne baki daya, amma ga yawancin al’ummar kasar nan ba a ga wani canji na a zo-a-gani ba. In kuwa har wadansu suka ce da mu ai an samu gagarumin canji, to sun tabbatar mana da yadda suke ganin Buhari da gwamnatinsa, wato tamkar tatsuniya ce da ake bai wa yara. Ina dalili?

Abubuwa uku zan kokarin fasaltawa domin mu ga hoton da kyau, wadanda da su ne aka yi wa al’umma babarodo domin zaben gwamnatin, amma ba ta sauya launi ba. Na farko an ce za a kawo tsaro a cikin kasa, a kuma tabbata an ci dunun Boko Haram da suka damke wuyan al’ummar Arewa maso Gabashin Najeriya da wasu sassa na Najeriyar baki daya. Lallai an samu shawo kan miyagun hare-haren da Boko Haram suka rika kaiwa a sassan kasar nan, amma shin an kawar da rashin tsaro da fargaba da tashin-tashina da kashe-kashe? Ko alama! Har yanzu sassan Arewa maso Gabas na fama da rashin tsaro, duk wanda ya ce an kawo karshen takaddamar Boko Haram to tatsuniyar Buhari ce yake saurare ba gaskiya ba. Baya ga wannan kuma, shin hare-hare da kashe-kashe da makiyaya da manoma ke ta faman yi, sun kau? Satar mutane fa? Fashi da makami fa? Shin mutanen da aka kashe a zamanin mulkin Shugaba Jonathan saboda rashin tsaro, sun fi na zamanin Shugaba Buhari ne ko kuwa an fi rashin tsaron a zamanin Buhari, kuma hasarar rayuka ta fi a  zamanin Buharin? Bude zuciya za a yi a fahimci lamurra ba ga-ta-ga-ta-nan ba in dai sauki da canji ake nema wa mutane!

Na biyu, shin talauci da fatara da yunwa da kunci da damuwa saboda tabarbarewar tattalin arziki a zamanin mulkin Buhari raguwa suka yi ko karuwa daga inda gwamnatin Shugaba Jonathan ta bari? Duk wadanda suka ce maka ai gwamnatin Buhari ta fitar da kasar nan daga husufin tattalin arziki wanda Jonathan da gwamnatin PDP ta sanya kasar nan a ciki, ce da su ta-zo-mu-ji-ta, in kuma har an yi hakan to ba bisa tsarin tattalin arziki ko wata manufa ta ciyar da tattalin arzikin gaba aka samu nasarar hakan ba, da jini da gumi da wahalar talakawa ne aka cimma haka. Tambayi kan ka don Allah, nawa litar man fetur take yau, za a ce da kai Naira 145, alhali a zamanin gwamnatin Jonathan tana Naira 87. Wadansu za su ce da ku an kara farashin albarkatun man fetur ne don a samar da shi a cikin kasa a kuma daina biyan tallafi da rara ga ’yan kasuwar da ke ci da gumin mutane. Amma hakan gaskiya ne? Ba gaskiya ba ne, domin har jiya har yau gwamnatin Buhari na biyan tallafi ga masu ci da gumin talaka, to ina amfanin badi ba rai!