✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Budurwar fitaccen mai gabatar da shiri za ta haifi dansa na 10

Shaharraren mai gabatar da shirin barkwanci a Amurka na ‘Wild N Out’, Nicholas Scott, wanda aka fi sani da Nick Cannon, ya ce yanzu haka…

Shaharraren mai gabatar da shirin barkwanci a Amurka na ‘Wild N Out’, Nicholas Scott, wanda aka fi sani da Nick Cannon, ya ce yanzu haka budurwarsa Brittany Bell na dauke da juna biyun dansa na 10.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, an gano shi a wurare da shiga daban-daban tare da Brittany din dauke da juna biyun da ya fara bayyana.

Yanzu haka dai yana da wasu ’ya’yan da suka haifa tare, wato Golden da aka haifa a 2017, da Powerful a 2020.

Wannan na zuwa ne bayan jaridar Daily Mail ta rawaito cewa wata budurwar tasa daban, Abby De La Rosa, wacce mahaifiya ce ga tagwayen ’ya’yansu, Zion da Zillion masu watanni 13, na da dauke da juna biyun dansa na 9.

Baya ga haka Nick na da wasu tagwayen ’ya’yan masu shekaru 11, wato Monroe da Moroccan da suka haifa da matarsa da suka rabu wato Mariah Carey.

Haka kuma akwai wani jaririn nasa da ya haifa da wata Bre Tiesi.

Sai dai mujallar Amurka ta US America ta rawaito cewa, wadannan ba su ne iya adadin matan da ya yi soyayya da su ba a rayuwarsa.

Domin kuwa akwai fitacciyar ’yar fin din Hollywood da suka fito tare a matsayin jarumai a wani fim dinsa mai suna’Love Don’t Cost A Thing’, wanda shi ne ya fito da shi duniya ta san shi, wato Christina Milan.

Haka kuma akwai shahararriyar ’yar Hollywood mai tada kura a duniya wato Kim Kardashian, tun kafin fara soyayyarta da tsohon mijinta Kanye West.

%d bloggers like this: