✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Budurwar da ta yada bidiyon tsiraicin babban jami’in gwamnati ta shiga hannu

Ta yada bidiyon da nufin tatsar Naira miliyan 15 daga hannun dan siyasar.

Jami’an tsaro sun gurfanar da wata buduwa a gaban kotu bisa zargin ta da yada bidiyon tsiraicin wani tsohon na kusa da Gwamnatin Jihar Bayelsa.

Ana zargin Charlotte Delhi mai shekara 19 da yada bidiyon da ya nuna tsiraicin Dokta Walton Liverpool a kafafen sada zumunta da nufin tatsar Naira miliyan 15 daga hannunsa.

Kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito, Mista Liverpool ya rike mukamin Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimin Jihar Bayelsa.

Kotu ta tuhumi Miss Charlotte da laifin yada hotunan tsiraici da nufin bata sunan Walton Liverpool, sai dai matashiyar ta musanta zargin da kotun ke mata.

Wani binciken jami’an tsaro ya nuna cewa layin da budurwar ta yi amfani da shi wurin yada bidiyon a WhatsApp na dauke da lambobin fitattun ’yan siyasa a Jihar Bayelsa.