✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budaddiyar wasika ga Ministan Abuja, Bala Muhammad

Ina fata kana cikin koshin lafiya, ina kuma fata za ka samu ikon karanta wannan wasika. Ni masoyinka ne, mai kuma burin ka zama Gwamna…

Ina fata kana cikin koshin lafiya, ina kuma fata za ka samu ikon karanta wannan wasika. Ni masoyinka ne, mai kuma burin ka zama Gwamna a Jihar Bauchi, sai dai tun kafin aje ko’ina na fara karaya da cewa anya za ka iya cika alkawuran da ka dauka?
Na fadi haka ne sakamakon rashin kammala wasan karshe na kofinka wanda aka yi wa taken kaura Unity Cup. Ina so na tunatar da kai (Bala Muhammad, kaura Bauchi) cewa an yi wasan kusa da na karshe tun saura sati daya a fara azumin bara, amma har yanzu ba a kai ga buga wasan karshe ba. Wannan zai iya sanyawa ’yan adawa su rika amfani da rashin yin wasan karshen wajen nuna cewa kai ba mai cika alkawari ba ne, wanda ni kuma ba zan so hakan ba, tun da a yanzu ma na fara jan daga daga wadanda suke goyon bayan wadansu ‘yan takarar.
A karshe ina fata za a gaggauta yin wasan karshen don na bayyana musu jinkiranka alheri ne.

Tambaya ga Oliseh Metuh na PDP
Editan Aminiya, ka ba ni dama in yi tambaya ga Kakakin Jam’iyyar PDP na kasa, ta yadda za a tantance wacce jam’iyya ke tauye hakkin al’umma da nakasa addininsu tsakanin PDP da APC?  Oliseh Metuh, ya zargi jam’iyyar adawa ta APC da cewa ta nuna fifiko ga wani addini, kasancewar shugabancin jam’iyyar ta APC ya kunshi Musulmi 18 da kuma Kirista 17. To amma ga shi gwamnatin jam’iyyar PDP ta kira taron kasa na mai wakilai 492, sai kuma taron ya kunshi Musulmi 183, Kirista kuma 383, sannan jama’ar Arewa 193, Kudancin kasa kuma mutum 300. Yaya ke nan Oliseh Metuh? Daga Mamman Lawan 08031867127

Tambaya ga Walid Jibrin
Assalamu alaikum. Ina son ku tambaya mini Walid Jibrin, don Allah Ya nuna mana jiha daya da PDP ke mulki, har ta yarda ta bar wa jam’iyyar adawa Shugaban karamar Hukuma daya a kasar nan. Mun tabbatar Gwamna Al-Makura na Jihar Nasarawa adali ne. Daga Yahaya Ango Gurku Karu, Jihar Nasarawa 07058978803.

Budaddiyar wasika ga Ahmad Mu’azu
Zuwa ga Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Ahmad Mu’az(Walin Bauchi). Mu matasan Jihar Bauchi muna kiran ka da ka zo Bauchi ka taimaki matasa, sakamakon rashin dogaro da kai. Rashin aikin yi babbar illa ce ga matasa, yakan sanya su shaye-shaye da sace-sace da kuma rashin samun ilimin addini da na boko, don haka ka zo ka taimaki matasa.  Za mu ci gaba da tunatar da ku ta kafafen yada labarai, don ku taimaki matasa. Daga karshe muna yi maka fatan alheri. Daga kungiyar Bobo Sita Youth Forum da ke Bauchi, 07037505701

Gwamnati ta tashi tsaye
Salam Aminiya ya kamata gwamnati ta tashi tsaye wajen maganin kashe-kashen da ake yi a Arewa; ga rikicin Fulani da Manoma; ga rikicin Boko haram. Tojama’a sai mu ci gaba da addu’a. Idan abu ya gagari gwamnati, ai ba zai gagari Allah ba. Allah Ka taimaki Najeriya da mutanenta. Amin summa amin. Daga Adamu Sulaiman Kaugama 08057672400.

Ga kungiyar KEKE-NAPEP
Assalamu alaikum. A gaya wa Shugabannin kungiyar Keke NAPEP, matakin da suke shirin dauka ba shi ne kasarmu Najeriya ke so ba. A dai yi adalci, don kada wankin hula ya kai mu dare. Daga Usman Bala Kagoro 07037084451.

Ga masu taron kasa
Assalamu alaikum. Don Allah Aminiya ku gaya wa masu taron kasa, cewa Najeriya kasa ce mai albarka da kima da daraja, ta kowane fanni da Allah Ya bai wa Musulmi da Kirista, ba kuma wanda zai kori wani daga cikinta. Kuma dunkulewarmu ita ce karfinmu. Don haka mu hada kai, mu gina kasarmu don mu ji dadinta. Addini kowa ya san wanda yake bi. Don haka sai a gano abin da zai hada kanmu, ba wargaza mu ba. Daga Murtala Isa Muhammad Ribe Kotorkoshi, mazaunin Abuja 08098964491.

Ina alkawari Kwankwaso?
A mika sakona ga Gwamna Kwankwaso, mutanen Kwanar dangora na cigiyarsa, a kan batun alkawarin da ya daukar musu, lokacin da aka taro shi daga kan iyakar Kano da Kaduna. Daga 08125555569.

Mu yi ta addu’a
Don Allah Aminiya ku jawo min hankalin manyan malamanmu na Najeriya, da su ja hankalin jama’a a gyara, a yi ta addu’a, har Allah Ya kawo mana karshen wannan musifar da ta addabe mu. Daga Zakiru Abubakar Jataka Kano, 08065946334.

Jaje ga masu sayar da waya
Edita ka isar min da jaje na ga masu sayar da waya a bakin bata, Bello Road, bisa gobarar da ta afku. Allah Ya kiyaye gaba. Daga Sunusi Musa Ciyaman Singa 08020800420.

Ana nuna wa Fulani wariya
Assalamu alaikum. Ami-niya, shin wai Fulani me ya sa duk abin da ya faru sai a ce su ne, me ya sa ake bambanta su da sauran kabilu? Daga Ibrahim Abuja. 08027666125

Kan T.Y danjuma
Kan T.Y. danjuma, Jarman zazzau, Malam Yasir Ramadan Gwale, duk da ra’ayinka ka fada, ba ka san irin alakar da ke tsakaninsa da mutane irin su Malam Aminu Kano da talakawan Arewa da ke Legas, bisa kyakkyawar tarbiyya da irin zamantakewa ta da. Ya kamata a rika tauna lafazi. Daga dan Malam T/Wada Jihar Kano 08022764659.

Ga Aminiya
A gaskiya Aminiya, mu ’yan Damaturu muna jin dadin karanta ki. Allah Ya kara wa Aminiya albarka. Daga Lawan A. Azeeko Damaturu 08038371816.