✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buba Galadima ya mayar da martani kan kwace kadarorinsa

A ranar Talata ne Hukumar da ke sanya ido kan masu taurin bashi AMCON ta Najeriya ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima. Rahotan na…

A ranar Talata ne Hukumar da ke sanya ido kan masu taurin bashi AMCON ta Najeriya ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima.

Rahotan na bayyana cewa, hukumar ta kwace kadarorin ne saboda tarin bashin da AMCON take bin fitaccen dan siyasar da suka kai kusan Naira miliyan 900.

Sai dai Buba Galadima, ya ce wannan umarnin kwace masa kadarori banbacin siyasa ne kawai.

A wata sanarwa da sashin watsa labarai na Hukumar sun fitar da sanarwar kamar yadda shugaban AMCON Mista Jude Nwauzor, ya fitar ranar Talata. Na cewa Buba Galadima da kamfaninsa Bedko Nigeria Limited, ya karbi rancen AMCON kusan Naira miliyan 900 daga bankin Eligible Bank Assets ta hannun bankin Unity Bank Plc a shekarar 2011. Ta ce, tun lokacin hukumar ta yi kokarin ganin an samu maslaha.

Amma Buba Galadima da kamfaninsa Bedko Nigeria Limited sun gaza biyan kudaden da hukumar ta ke binsu.

Gwamnatin tarayyar Najeriya a shekarar 2019 ta sanar da cewa ba zata sake yin kasuwanci da wadanda suka ranci kudaden AMCON ba, har sai sun biya bashin da ake binsu.

Kimanin Naira miliyan 5 AMCON ke bin wasu da suka karbi rancen kudi basu dawo da su ba.

A rahoton BBC Hausa, wata babbar kotu a Abuja, ce ta umarci Hukumar AMCON da kwace kadarorin.

Umarnin kotun wanda mai shari’a A.I Chikere, ya zartar da shi ya bai wa hukumar damar ta kwace ragamar kadarorin na dan siyasar.

Kadarorin da aka kwace sun hada da gida mai lamba 15 a Addis Ababa Crescent da ke Wuse Zone 4 a birnin Abuja da kuma gida mai lamba 4 a Bangui Street, Wuse 2 shi ma a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaban AMCON, Jude Nwauzor ya ce hukumar za ta dauki duk matakan da suka kamata kan kamfanin Bedko Nigeria Limited da kuma daraktocinsa bisa hukuncin kotun da kuma dokokin hukumar da aka yi wa gyaran fuska.

Sai dai tuni Buba Galadima ya mayar da martani inda ya fada wa BBC cewa wannan lamari na da nasaba da takaddama kan wani bashin banki wanda ya shafi wata kwangilar sayen taki da gwamnatin jihar Kano ta ba shi a shekarar 2003.

Ya ce, “Ni ne na samu kwangila ta kawo taki a zamanin Gwamna Ibrahim Shekarau a 2003, da aka bani kwangila na je bankin Tropical Commercial Bank na nemi a bani kudi bashi na kawo kayan.

“Ban karbi kudi a wajensu ba, kudinsu yana gunsu, duk inda na je neman kaya sai a ce ba za a karbi takardar bashi daga bankin ba domin bankin ya na da matsala da hukumar Amurka,” in ji Buba Galadima.

“An yi haka har shekara uku, ni ban karbi ko kwabo ba, su ake bude takardar bashi a wurinsu, a dalilinsu ne aka ki karbar kudin nan domin ai ba wanda za ka je wurinsa yana da kayan sayarwa da kudinka, ya hana ka.” kamar yadda Buba Galadima ya fada.

Ya ce, daga baya bankin Tropical ya aiko masa da bill cewa kudin ruwa ya taru na Naira miliyan 349 “suka tafi kotu a kan a tilasta ni na biya wadannan kudade.”

A cewarsa, “Babu abin da na bayar ajiya idan an biya saboda yarjejeniyarmu da shi shi ne idan kaya ya zo za a biya kudin kayan ta hanyarsu, toh tun da kaya bai zo ba, shi ne suka shigar da kara cewa na biya kudin.”