✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buba da Ilu (1)

Buba da Ilu Hadejawa ne abokan juna amma Buba attajiri ne, sai ya biya wa Ilu Makka. Bayan ya dawo aikin Hajji, sai ran nan…

Buba da Ilu Hadejawa ne abokan juna amma Buba attajiri ne, sai ya biya wa Ilu Makka. Bayan ya dawo aikin Hajji, sai ran nan suka bata har Ilu ya zagi Buba, sai Buba ya ce: “Tun da ka zage ni, na amshe Makkata, kai yanzu ba Alhaji ba ne, kada a kara kiranka Alhaji, kada ka sake amsawa, daga yau na hana.” Sai wani Bakatsine ya ba Buba hakuri, sai ya ce: “Na hakura, na yafe masa, na maida masa Makkarsa, ku ci gaba da kiransa Alhaji. Dama bacin rai ne.” Sai Ilu ya yi ta godiya.
Daga Amiru Isa Bakori, 07068147933