✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe mutum 69 a Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe mutum 69 a jihar Borno kwana biyu bayan Babban Hafsan Mayakan Kasa Tukur Buratai ya bar jihar inda ya jagoranci…

Mayakan Boko Haram sun kashe mutum 69 a jihar Borno kwana biyu bayan Babban Hafsan Mayakan Kasa Tukur Buratai ya bar jihar inda ya jagoranci yaki da kungiyar.

Maharan sun shafe awa biyu suna cin karensu babu babbaka da tsakar rana a kauyen Foduma Kolomaiya da ke Karamar Hukumar Gubio.

Mazauna sun ce maharan sun sace dabbobi kusan 1,000 baya ga wasu 300 da suka karkashe.

Majiyarmu ta ce harin na ranar Talata ya zo ne kwana guda bayan ‘yan Boko Haram sun tare matafiya a kan babban titin Monguno, inda suka jikkata mutane da dama.

Wakilinmu bai samu jin ta bakin Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Kanar Sagir Musa ba game da lamarin, duk da kokarin da ya yi na tuntubar sa har zuwa 10.09 na daren Talata.

Duk da haka jami’ai a wata babbar hukumar kasashen duniya da ke aiki a jihar Borno da ‘yan sintiri sun tabbatar da harin na Gubio.

“Shi ne hari mafi muni a ‘yan kwanan nan. Nisan kauyen ya sa ba za a iya kai musu agaji ba a kan kari”, inji jami’in.

“Sun kashe mutane da yawa wasu kuma sun bace kasancewar da tsakar rana suka kai harin”, inji wani jami’in.

Dan sintirin ya ce sun kirga gawa 69. “Bacin wadanda ba a gani ba ke nan…Zuwa gobe (yau) za a samu karin bayani a kan harin”, inji shi.

Janar Tukur Buratai ya bar jihar Borno ranar Lahadi ya ce sojoji na samun gagarumar nasara a yaki da suke ci gaba da yi da kungiyar.

A jawabinsa ga Shugaba Buhari a Abuja ranar Litinin, Buratai ya ce a tsawon zamansa sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 1,429, sannan suka kame wasu 116.