Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne yanzu haka na can suna cin karen su ba babbaka a garin Garkida da ke Karamar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.
Wakilinmu ya ce maharan sun mamaye garin ne ta babbar mashigar sa da yammacin ranar Alhamis, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankunan guduwa zuwa tsaunukan da ke makwabtaka da garin domin tsira da rayuwar su.
- Boko Haram: An kashe sojoji 5, an sace fararen hula 35 a wani sabon hari
- Mayakan Boko Haram sun yi wa Fasinjoji kofar-rago a Konduga
“Na gan su a kan motoci biyar suna tunkarar garin, daga bisani kuma na jiyo karar harbe-harbe mutane kuma suka fara guduwa zuwa tsaunuka,” inji wani mazaunin garin da ya gudu.
Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu cikakken bayani kan harin ba.
Kazalika, har yanzu jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba a hukumance a kan harin.
Jihohin Borno, Yobe da Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas sun jima suna fama da rikicin da ke da nasaba da ta’addancni Boko Haram, lamarin da alkaluma suka nuna ya yi sanadiyyar kisan sama da mutane 200,000 tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu.