✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram sun kashe manoma 4 da kona gawarsu a Borno

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kaiwa gonakin shinkafar unguwannin Zabarmari da Koshebe a yammacin ranar Asabar yayin da suka kashe manoma…

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kaiwa gonakin shinkafar unguwannin Zabarmari da Koshebe a yammacin ranar Asabar yayin da suka kashe manoma 4 da kuma kona gawarwakinsu.

Unguwannin sun kai nisan kilomita 10 zuwa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Wadanda ake zargin a ranar 1 da Disamba sun kai hari gonakin shinkafa inda suka lalata hekta-hekta na gonakin shinkafar wadanda aka girbe.