✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram na sace ɗanyen abinci a gonaki —Ndume

Sun addabi al'ummar yankunan Karamar Hukumar Gwoza da sace danyen amfani a gonaki

Mayaƙan Boko Haram sun koma sace ɗanyen amfanin gona a gonakin jama’a a yankunan Jihar Borno.

Sanata Ali Mohammed Ndume ya ce sace ɗanyen amfanin gona da mayaƙan da suke yi ya kawo babban cikas ga harkokin tattalin arziki al’ummar yankunan Karamar Hukumar Gwoza.

Ya ce ayyukan kungiyar na ci gaba da barazana ga al’ummaomin ’yan gudun hijira da aka mayar da su garuruwansu na Ngoshe, Kirawa, Warabe, Wala, Pulka da ma garin Gwoza, fadar karamar hukumar.

Ndume ya ce har yanzu mayaƙan kungiyar suna addabar al’ummomin yankunan Gwoza da ke makwabtaka da Jamhuriyar Kamaru.

Don haka, ya yi kira ga sojoji da su kara azama wajen murƙushe ragowar mayaƙan ƙungiyar a yankin Dajin Sambisa da Tsaunin Mandara.

Wannan korafi da Ndume ya yi kan sace amfanin gona da bai kosa ba na zuwa ne bayan wani ƙazamin hari da kungiyar ta kashe mutane 87 a Jihar Yobe, makwabciyar Borno.