✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biyan halattattun bukatun malaman makaranta

Kwananin baya ne kungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen Birnin Tarayya ta umarci mambobinta kan su fara yajin aikin sai baba ta gani bisa…

Kwananin baya ne kungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) reshen Birnin Tarayya ta umarci mambobinta kan su fara yajin aikin sai baba ta gani bisa zargin gazawar Hukumar Birnin Tarayya (FCTA) na cika musu wasu alkawura bayan cikar mako biyu na wa’adin da ta diba mata. kungiyar ta bukaci Hukumar FCTA ta dawo da biyan albashin malamai 3,000 ga mambobinta kuma ta dakatar da bincike marar ma’ana da ta dauki dogon lokaci tana don tantace malaman kuma ta saki takardar karin girma na malaman na baya-bayan nan.

Duk da cewa an dakatar da yajin aikin jim kadan da fara shi sakamakon sanya bakin Ministan Birnin Tarayya Alhaji Bala Mohammed, matsala ce mai dogon tarihi kuma ta dade tana cutar da malaman da dama musamman a matakin farko na bangaren ilimi na kasar nan.
Malaman makaranta a Jihar Benuwai kwanakin baya sun fada kan titunan Makurdi suna zanga-zanga kan zargin kin aiwatar musu da sabon tsarin albashi na kasa. Lokacin da yake musanta da’awar malaman Mai taimaka wa Gwamnan Benuwai kan harkokin kananan hukumomi da al’amuran masarautu Mista Sololmon Wombo ya ce ‘malaman ba su bin gwamnati koda kwabo.’
Malaman makaranta a Jihar Kuros Riba ma suna fama da nasu matsalolin. Sun nuna matukar bacin ransu lokacin da Gwamna Liyel Imoke ya ce karin kashi 27 da rabo cikin 100 ga malaman da aka cimma yarjejeniya shekara goma baya rashin kan gado ne kuma ba za a biya su ba.
Bukatar sabon tsarin albashin malaman makaranta (TSS) da aka faro a 1992, sai a shekarar 2003 Gwamnatin Tarayya ta amince da shi. Kuma sabon tsarin na TSS shi ne karin kashi 27 da rabi da za a kara ga albashin malamai amma ya ci gaba da zama matsalar da jihohi da dama ke jan kafa a kai.
Wannan rashin imani na kula da jin dadin malamai shi ke haifar da koma bayan ilimi kamar yadda ke bayyana ta wajen gagarumar faduwa a jarrabawa da rashin daidaiton kalandar karatu. A baya lokacin da abin alfahari ne a ce kai malamin makaranta ne, ba a bullo da muguwar dabi’ar nan ta neman kudi da ake kira darussan bayan makaranta ba a makarantun firamare da kananan sakandare, saboda malaman suna sadaukar da kai ga ayyukansu. Albashi yana da auki kuma martabar da gwamnati da jama’a ke ba malamai tana da yawa.
Abin takaici ne yadda gwamnati a matakin tarayya da jihohi da kananan hukumomi suke sakaci a wannan bangare duk da cewa ilimin firamare yana da muhimmanci ga samun nasarar sauran matakan. Yin sakaci ko gazawar masu ruwa da tsaki a daidaikunsu ko a hade wajen ba ilimin firamare kular da ta kamata tabbatacciyar hanya ce ta ruguza daukacin tsarin ilimin.
Inganta jin dadin rayuwar malaman makaranta ba ma kawai kashin bayan cimma nasara da manufofin da ke kunshe a Tsare-Tsaren Ilimi na kasa ba ne, har ma ta zamo hanyar da ta saura na ci gaba da rike kwararrun malamai su ci gaba da aikin. Galibin wadanda suke da kwarewa a fannin koyarwa suna aikin koyarwa ne a matsayin na wucin gadi kafin su samu aikin da ya fi albashi mai gwabi.
Domin a maganace wannan rikici a matakin makarantun firamare akwai bukatar a sake nazarin tsarin ilimin koyarwa na kasar nan. Rushe kwalejojin horar da malamai hakika ya kara cukurkuda kalubalen da banagren ke fuskanta. Horar da masu takardar koyarwa ta NCE ba ta dace da abin da ake fata daga gare su ba a makarantun firamare inda takardun NCE ne mafiya karancin takardar kwarewa don koyarwar. Kuma a yayin da kwalejojin horar da malamai suke tattalar daliban da suke yayewa don su koyar da kusan dukkan darussa a makarantun firamare, shirin NCE ya fi takaitawa kan darussa biyu ne kawai, manufa shirin na bukatar karin malamai a matakan firamare a lokacin da babu wadatattun masu takardar NCE da za su wadaci koda makarantun sakandare da ake da su. Domin a magance wannan tasgaro, wajibi ne gwamnatocin jihohi su karbo kudin hadin gwiwa na shirin UBE da Babban Bankin Najeriya ya sha nanata cewa suna nan jibge a asusunsa ba a karba ba kuma su karfafa wa kananan hukumomi su cimma duk kudirorinsu a wanan fanni. Kuma wajibi ne ma’aikatun ilimi na jihohi su farfado tare da karfafa sassan duba malamai domin tabbatar da ingancin aikinsu da tabbatar da suna bin ka’idojin da ke cikin manhajar ilimi.