Gwamnonin Jihohin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun nesanta kansu daga masu fafutukar ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biyafara.
Sun kuma yi Allah-wadai da hare-haren da suka biyo bayan fafutukar, wadanda suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.
- Masu kai wa ’yan bindigar Kaduna burodi sun shiga hannu
- Amina Mohammed ta sake zama Mataimakiyar Sakatare Janar na MDD
Idan dai za a iya tunawa, haramtacciyar kungiyar nan ta ’yan awaren Biyafara ta IPOB ta jima tana kokarin ganin yankin ya balle daga Najeriya.
To sai dai Gwamnonin sun yi wani taro a Enugu ranar Asabar domin tattauna matsalolin da suka addabi yankin da kuma hanyoyin lalubo bakin zaren.
Shugaban Gwamnonin, kuma Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi wanda ya yi magana a madadin takwarorin nasa ya ce, “Muna Allah-wadai kan dukkan abubuwan da masu fafutukar nan suke yi na tada-zaune-tsaye, ko a Kudu maso Gabas ko ma a kowanne yanki.
“Muna jaddada cewa mana tare da su, ba da yawunmu suke yi ba.
“Zargin da ake yi cewa jagororin wannan yankin sun yi gum da bakinsu a kan lamarin ba gaskiya ba ne.
“Mu ’yan kabilar Ibo, muna jaddada mubayi’armu ga Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya, wacce za a tabbatar da adalci, ’yanci, soyayya da kaunar juna a cikinta,” inji Gwamnonin.