✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biri ko mutum?

Wata mata ta shiga tasi sai ta zauna gidan gaba, ana cikin tafiya sai direban ya juyo ya kalle ta da ita da yaronta, sai…

Wata mata ta shiga tasi sai ta zauna gidan gaba, ana cikin tafiya sai direban ya juyo ya kalle ta da ita da yaronta, sai ya kwashe da dariya ya ce: “Gaskiya Hajiya ban taba ganin mummuna irin yaronki ba.” Ta dube shi ta yi tsaki, sannan ta ce ya tsaya ta koma baya. Ta koma baya tana zage-zage, sai wani tsoho da ke bayan motar yake tambayarta abin da ya faru, sai ta fada masa abin da direban motar ya ce mata. Tsohon ya ce: “Kin mare shi?” Sai ta ce: “A’a.” Sai ya ce: “Kawo birin da ke hannunki, in rike maki shi, ki je ki mare shi.” Jin haka, tuni zuciya ta kashe ta, ta dankara wa tsohon nan mari, saboda ya kira danta da biri.

Daga Buhari Liman Kudan, 08034500055