✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon Shekau kalubale ne ga musulmi – Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci

Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ta bayyana bidiyon Shugaban Kungiyar  Boko Haram, Abubakar Shekau na baya-bayan nan a matsayin babban kalubale ga al’ummar…

Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ta bayyana bidiyon Shugaban Kungiyar  Boko Haram, Abubakar Shekau na baya-bayan nan a matsayin babban kalubale ga al’ummar Musulmi.

Majalisar ta kuma kalubalanci Abubakar Shekau ya fito fili ya daina boye kansa ga jami’an tsaro.

Babban Sakataren Majalisar Dokta Nafi’u Baba Ahmad ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a Kaduna, inda ya  ce wannan bidiyo ya kara tabbatar da cewa batun tsaro akwai matsala a kasar nan.

Dokta Nafi’u Baba Ahmad ya ce majalisar ta lura cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kokari a batun yaki da ta’addanci amma ga dukkan alamu abin na neman dawowa. “Abin a yaba ne a lokacin, amma a yanzu saboda masalolin tsaro ’yan ta’adda na neman dawowa wanda kuma abin bakin ciki ne,” inji shi.

Idan ba a manta ba Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo yana barazanar cewa za su yi maganin Ministan Sadarwa Dokta Isa Ali Pantami kan kokarinsa na dakile ayyukansu ta rage yawan layukan sadarwa a kasar nan.

Sannan Shekau ya tunatar da Ministan kan yadda aka kashe Sheikh Jafar Mahmu Adam a shekarar 2007, sannan ya ce duk inda mutanensa suka yi arba da Dokta Pantami shi ma a kashe shi.

Shekau ya kuma yi barazana ga Barisa Bulama Bukarti wani mai bincike kan ayyukan Boko Haram da ke karatu a kasar Ingila a yanzu, kuma ya yi barazanar daukar mataki a kan kafofin  watsa labarai na ciki da wajen Najeriya.