Aminiya ta gana da Attah Tambari, shugaban bikin Bianou na birnin Agadez, inda ya yi tsokaci kan mashahurin bikin al’ada da Abzinawa ke gudanarwa a kowace shekara cikin watan cika-ciki, wato Muharram a kidayar watannin Musulunci. Ga dai yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za ka iya bayyana mana shekarunka na haihuwa?
Tambari: Hakikanin gaskiya ba zan iya tantance shekaruna ba, amma ina tunanin ko 70 ko 75. Babban dai abin da na sani shi ne tsohon Sarki, baban wannan na yanzu ya nada ni shugaban Bianou, kimanin shekara 40 da ta wuce.
Aminiya: Mece ce ma’anar Bianou a harshen Abzin?
Tambari: Bianou a harshen Abzin tana nufin ‘Safiyar rawa,’ (wato rawa ce da ake farawa da dare, kuma ba a dainawa har sai gari ya waye).
Aminiya: Shin Bianou al’ada ce ko addini?
Tambari: Bianou al’ada ce wadda muka gada iyaye da kakanni.
Aminiya: Yaya ake gudanar da bikin Bianou?
Tambari: Bayan layya, wato daga ranar 17 ga watan Zul-hijja, har wata ya kai 30 ana shirye-shirye. Da sabon wata ya kama an fara wasanni ke nan har zuwa takwas ga watan Muharram. Daren 9, sai a nufi Aleksis (wani kauye ne a cikin daji). Safiyar tara ga wata, sai mu taso da safe, mu biyo hanya, daga nan za mu shigo gari, ta bakin soja, mu biyo Marie (Ofishin Magajin gari), sai gidan Gwamna; daga nan sai Tudun-kasa; sai gidan Sarki; sai gidan dangaladima; sai gidan Turawa; sai mu sake dauko wata hanyar zuwa gidan alkali zuwa gidan Alamu; sai gidan An Tala. Daga nan sai gidan Dije, inda samari ke shan ruwa.
’Yan zirya (masu rawa) sai a nufi Fumiyemari (unguwa) zuwa Amarewai daga nan sai Umurda-Magas; sai Bangon moli. Daga nan sai mu gangaro a Kanfaya; sai Anasakindai; sai gunsun Mudin nafalla daga nan sai unguwar baya; sai gidan Kundi (wata mace ce), inda a nan ake yada Bianou.
Aminiya: Jaridarmu ta samu labari an yi fada tsakanin Abzinawan Gabas da na Yamma, ko me ya kawo rikicin?
Tambari: A’a, a da ne gasar take zama da gaba, amma yanzu gaba ta tashi. Kuma a da da wuya a tashi, in an gama sai an yi fitina. Kuma (mu ’yan Gabas), ai da ma mun fi su yawa. Yanzu kuwa tubarkalla, sun samu mutane. Abin dai ba irin na da ba ne, domin sun sami jikokin kakansu, har da Agwalla Yamma (Sarkin Samari) da jarumi tambari da masu rike tambura da masadayya (abin bugu).
Aminiya: Mene ne bambancin bikin Bianou a da, da yanzu?
Tambari: A da, yaro karami ba ya kada akazam (dan karamin mandiri). ’Yan mata kuwa sai su taru wuri guda. Kuma samari ba ruwansu da ’yan mata har sai an yada Bianou. Kuma komai kankantar yaro, sai an yi masa rawani zai fita Bianou. ’Yan mata su sanya zulumbu.
Aminiya: Wacce shawara za ka bai wa matasa a kan Bianou?
Tambari: Samari su yi kokari kada su yada Bianou, domin shi kadai ya rage mana na al’ada. Idan suka yada ta, to ta lalace musu, kuma Agadas ta baci.
Bianou na nufin rawar da sai gari ya waye – Attah Tambari
Aminiya ta gana da Attah Tambari, shugaban bikin Bianou na birnin Agadez, inda ya yi tsokaci kan mashahurin bikin al’ada da Abzinawa ke gudanarwa a…