✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bello Maitama Yusuf ya rasu

Allah ya yi wa Sardaunan Dutse, Sanata Bello Maitama Yusuf rasuwa da safiyar Juma’a a Kano. Marigayin ƙwararran lauya ne wanda ya yi minista a…

Allah ya yi wa Sardaunan Dutse, Sanata Bello Maitama Yusuf rasuwa da safiyar Juma’a a Kano.

Marigayin ƙwararran lauya ne wanda ya yi minista a jamhuriya ta biyu kuma ya zama sanata a jamhuriya ta huɗu.

Ya rasu ya na da shekaru 76 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Mutum 20 da Shata ya fito da su a waka

Ya bar mata biyu da ƴaƴa 10, maza biyar, mata biyar.

Za a yi jana’izarsa bayan Sallar Juma’a a Fadar Sarkin Kano.