✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shafe kwanaki ana kokarin ceto shi, yaron da ya fada rijiya a Maroko ya rasu

Ma’aikatan kwana-kwana suka rika aiki ba dare ba rana wajen kokarin ceto shi.

A kasar Maroko, murna ta koma ciki bayan da aka tabbatar cewa yaron nan mai shekara biyar da aka shafe kwana hudu ana kokarin ceto shi daga wata tsohuwar rijiyar da ya fada, Rayan Oram, ya rasu.

Yaron dai ya fada rijiyar ne ranar Talata, yayin da ma’aikatan kwana-kwana suka rika aiki ba dare ba rana wajen kokarin ceto shi.

Mutanen kasar dai sun yi ta murna bayan da aka samu ceto Rayan da yammacin Asabar, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu.

A shafin Twitter dai, inda maudu’in #SaveRayan ya rika yin tashe musamman a kasashen Larabawa, jim kadan da bullar labarin rasuwar tashi mutane suka shiga aike wa iyalansa da sakon jaje, da kuma jinjina wa ma’aikatan ceton.

Mahaifiyar Rayan ta shaida wa gidan talabijin na Aljazeera a wurin aikin ceton cewa ta sha yin addu’ar ganin an ceto shi da rai.

Imad Fahmy, wani mai aikin sa-kai da kungiyar ba da agaji ta Red Crescent a kasar ya ce da farko yaron ya dan fara shakar iska, kafin rai ya yi halin nasa daga bisani.

Ma’aikatan ceton dai sun samu damar jona wa Rayan iskan shaka ta oxygen ta hanyar wata kafa a cikin rijiyar, sannan aka saka kyamarar da ta rika daukar hoton yadda yake a ciki.

Sai dai aikin kokarin yashe rijiyar ya ci tura, lamarin da ya sa ala tilas aka koma amfani da diga da shebur wajen aikin yashe rijiyar.

Tuni dai Sarkin kasar ta Maroko, Mohammed VI, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyayen yaron ta wayar salula.

Wasu hotuna a kafafen sada zumunta sun nuna gawar marigayin nade a cikin wani kyalle mai launin ruwan dorawa, bayan an ciro shi ta wata kofa da aka haka a rijiyar.