Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar Kano a ranar Litinin don kaddamar da manyan ayyuka takwas da Gwamnatin Jihar da ta Tarayya suka aiwatar a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar, ta aike wa Fadar Shugaban Kasa takarda kan bukatar a dage ziyarar ta Buhari duba da matsin rayuwa da sauya sabbin kudi ya haifar da kuma matsalar tsaro.
Sai dai Babban Bankin Najeriya (CBN), ya bayyana kara wa’adin kwana 10 na daina amfani da tsofaffin takardun kudi.
Aminiya ta ruwaito yadda shugaban ya dage kan cewar sai ya ziyarci jihar don kaddamar da ayyukan kamar yadda aka tsara.
Hadimin Shugaban Kasa kan kafafen zamani, Bashir Ahmad ya bayyana cewar ziyarar ta Buhari a ranar Litinin tana nan daram.
“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zo a ranar Litinin don kaddamar da ayyukan Gwamnatin Tarayya da na Jiha. Idan gwamnati tana ganin babu tsaro game da ziyarar Shugaban Kasa, to zai kaddamar da ayyukan gwamnatin tarayya, amma zuwansa na nan ba fashi.”
Sai dai a ranar Lahadi, Gwamnatin Kano ta ce ta kammala shirye-shiryenta don tarbar Shugaba Buhari a ranar Litinin da zai kaddamar da ayyuka takwas a Jihar.
A cikin wata sanarwa ranar Lahadi, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba, ya ce Ganduje da mukarrabansa sun shirya tarbar Buhari.
A ranar Lahadi ne, Ganduje ya ziyarci Buhari a gidansa da ke Daura don tattaunawa game da ziyarar Shugaban zuwa Jihar, sai dai babu wani cikakken bayani kan abin da suka tattauna yayin ganawar tasu.