✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan bukatar ‘Yan Majalisa: Buhari na gana wa da hafsoshin tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na gana wa da hafsoshin tsaron kasar a fadar gwamnati da ke Abuja. Rahotanni na bayyana cewa, manyan jami’an tsaron da…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na gana wa da hafsoshin tsaron kasar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Rahotanni na bayyana cewa, manyan jami’an tsaron da suka halarci ganawar sun hada da:  Sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha da shugaban ma’aikata ga shugaban kasa, Abba Kyari da Ministan tsaro Manjo Janar, Bashir Salihi Mahashi (mai ritaya) da Ministan Harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da kuma  mai  bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Babagana Monguno.

Hafsoshin tsaron da suka halarci ganawar su ne Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Gabriel Olonisakin da hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai da hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da hafsan sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar da kuma sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.

Yayin da sauran kuma sun hada da: Darekta Janar na hukumar leken asiri ta (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar da Darekta Janar na hukumar tsaro ta farin kaya, (DSS), Yusuf Magaji Bichi.

Sai dai a ba sanar da dalilin taron da shugaban ya yi da hafsoshin tsaron ba. Amma ana alakanta taron da bukatar da ‘yan Majalisar dokokin Najeriya suka yi ta yi a ranar Laraba kan tabarbarewar harkar tsaron Najeriya, inda wasu suka bukaci da a cire hafsoshin tsaron kasar.