✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bawan Allah

Wani dantibi ne ya musulunta sai ya zabi a sanya masa sunan Aliyu. Rannan ya je wurin wa’azi sai ya tarar ana ba da sadaka,…

Wani dantibi ne ya musulunta sai ya zabi a sanya masa sunan Aliyu. Rannan ya je wurin wa’azi sai ya tarar ana ba da sadaka, shi ma ya ba da sadakar Naira dari biyu. Mai gabatarwa ya ce: “Wani bawan Allah ya ba da sadaka, Allah Ya saka masa. Da jin haka sai dantibi ya dawo wurin mai gabatarwa ya ce: “Ba bawan Allah ba ne, ni ne Aliyu dantibi!”

Daga Umar Saleh Gora, 08126035717