✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun yajin aikin likitocin Najeriya

kungiyar Likitoci Ta Najeriya ta tsunduma cikin yajin aikin gargadi a duk fadin kasar nan a Larabar da ta gabata tare da neman Gwamnatin Tarayya…

kungiyar Likitoci Ta Najeriya ta tsunduma cikin yajin aikin gargadi a duk fadin kasar nan a Larabar da ta gabata tare da neman Gwamnatin Tarayya ta biya musu bukatunsu.
Wannan yajin aiki, wanda ya maye gurbin shigensa da kungiyar Likitoci ’Yan kasa suka yi na tsawon makonni uku, wanda suka karkare a kwanakin baya, lallai zai kara ta’azzara matsalolin kiwon lafiya a kasar nan. A wannan karon, kungiyar Likitoci Ta Najeriya ta ce ba ta da zabi sai ta shiga yajin aikin saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika alkawarin yarjejeniyar da suka kulla da juna.
Likitocin sun dora laifi ga Ministan Lafiya, Dokta Onyebuchi Chukwu bisa ga gazawarsa, sannan suka ce duk wata matsala da za ta biyo baya a kasar nan sakamakon yajin aikinsu, to shi za a zarga da laifi.
A yayin da kasar nan ta koma gidan yaje-yajen aiki, a wannan karon, bai kamata kuma a ce an kara saka al’umma cikin wani yajin aikin da ya shafi harkar lafiya ba. Don haka ya dace duka bangarorin biyu, likitoci da Gwamnatin Tarayya su yi kokarin shawo kan al’amarin.
Kamar bangaren ilimi, bangaren lafiya ma ya jigata sosai a sakamakon yaje-yajen aiki. ’Ya’yan kungiyar Likitoci Ta Najeriya na sassa daban-daban kasar nan sun sha shiga yaje-yajen aiki a lokuta daban-daban, kamar kuma yadda takwarorinsu na kungiyar Likitoci ’Yan kasa da kungiyar Nas-Nas Da Unguwar Zoma Na Najeriya da sauransu suka rika yi.
Kamar yadda Shugaban kungiyar Likitoci Ta Najeriya, Dokta Osahon Enabulele ya bayyana a wani jawabi nasa dangane da yajin aikin, ya ce a ba, abu guda daya ne kacal cikin abubuwan da suka yi yarjejeniya da gwamnati aka cika masu. Wannan bukata da aka biya masu guda daya kuwa ita ce, sake fasali da tsarin Hukumar Ma’aikatan Lafiya Da Na Hakori. Ya yi koken cewa sauran bukatun da suka nema kuma aka amince a yarjejeniyarsu da gwamnati, an yi watsi da su. Bukatu kamar wadanda suka danganci kyautata wuraren da suke aiki da kuma rashin adalci da zaluncin da ake yi wa likitoci ta bangaren yanayin aikinsu. Haka kuma akwai bukatar ingantawa da samar da kayan aiki na zamani da kuma batun samar da isassun kudin gudanarwa ga sashin lafiya.
Shugaban likitocin kuma ya bayar da misalan tarukan da suka yi ta yi da jami’ai da hukumomin gwamnati, tsawon watanni biyar da suka gabata. Irin wadannan taruka, sun hada da wanda suka yi da Ma’aikatar Lafiya Ta Tarayya da Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Shugaban Ma’aikata na Najeriya. Ya kara da cewa, dukkan wadannan taruka da suka gudanar, ba su haifar da wani abu mai muhimmanci ba, sun tafi a banza.
Ita bangaren gwamnati, ba ta yi bayanin abin da ya hana ta biya masu bukatun nasu ba amma koma dai yaya ne, tun da farko bai kamata gwamnati ta bari wannan yajin aiki ya wakana ba, domin kuwa barnar da zai ci gaba da haifarwa ba mai dadin ji ba ce, musamman ma idan aka yi la’akari da yanayin da kasar nan ke ciki.
Wani abin mamaki kuma shi ne, wane dalili ne ya sa likitocin suka dora laifin matsalarsu ga Ministan Lafiya shi kadai? Enabulele bai bayar da wani karin bayani ba, kodayake abu ne da aka saba da shi, masu yajin aiki su ta’allaka laifi ga minista, musamman idan al’amarin ya shafi kyautata wa ma’aikata. Haka al’amarin yake, idan aka duba hukumonin ilimi da na lafiya.
A ganinmu, akwai matsalar rashin tuntuba da bayani tsakanin kungiyar Likitoci da Gwamnati, domin tattaunawa yadda za a magance matsaloli da bukatun nasu cikin ruwan sanyi, ba tare da an shiga yajin aiki ba. Ita kanta gwamnati, tana da laifi, saboda ta yi kaurin suna wajen saba alkawari kan yarjejeniyar da take daukar alkawari da ’yan kwadago. Ya dace a duba wannan, domin a lokacin da aka karya alkawari, wannan kan iya haifar da rashin aminci tsakanin juna.
Abu ne mai muhimmanci ga Ministan Lafiya ko kuma wani wakilinsa ya bi duk hanyar da ya kamata ya bi domin ganin an kawo maslaha da sasanci tsakanin gwamnati da kungiyar Likitocin Najeriya, domin a dakatar da yajin aikin nan. Ya kamata su kuma likitocin su saurari gwamnati, su ji matsayarta kan lamarin, su kula da raunana, marasa lafiya da yajin aikin nan yake shafa.