✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun hadewar jam’iyyun adawa da canja sheka

A can baya, jam’iyyar PDP ta sha gamuwa da matsaloli da rikice-rikice kuma ta wanye da su lafiya, sai dai kalubalen da ke fuskantar jam’iyyar…

A can baya, jam’iyyar PDP ta sha gamuwa da matsaloli da rikice-rikice kuma ta wanye da su lafiya, sai dai kalubalen da ke fuskantar jam’iyyar wacce ake wa kirari da mafi girma a Afrika mai girma ne, wanda ya wuce misali.
A makon jiya ne gwamnoni biyar daga cikin bakwai da ke kiran kansu da sunan ’ya’yan sabuwar PDP suka sanar da canja sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC, wacce ita ma hada kan wasu jam’iyyu ce. Jiga-jigan jam’iyyar PDP sun fito fili suna nuna rashin damuwarsu da abin da ya faru, amma a boye babu shakka suna cikin turaddadi da tsoro, musamman saboda sun kwana da sanin rashin da suke fuskanta; musamman ma ganin cewa zabe na karatowa a 2015. Babu shakka, dole ne PDP ta nuna damuwa da rasa gwamnoninta biyar, balle kuma akwai yiwuwar ta kara rasa wasu nan gaba. Idan a can baya tana tokabo da yawan gwamnoni 23, yanzu sun dawo 18, a yayin da APC ke da 16, LP tana da daya, ita ma APGA tana da daya. Ke nan, idan aka hada jam’iyyun adawar a wuri daya, suna neman yin kan-kan-kan da PDP, kuma akwai yiwuwar ta rasa kima a Majalisun Tarayya. Wannan yana nuna cewa lallai jam’iyyun adawa sun samu karsashi kuma idan suka hada kai sosai, za su iya karya lagon PDP. Haka kuma, al’amarin ya kawar da tsoron da wasu ke yi, na maida kasar nan mai jam’iyya daya.
Wani abu kuma da za a yi la’akari da shi, shi ne yadda gwamnoni ke da tasiri da karfi a jihohinsu, musamman idan ana batun zabe, wanda haka ke nuna cewa lallai PDP za ta fuskanci faduwa, domin kowane gwamna zai tabbatar da cewa ya cinye zaben jiharsa. Idan muka duba abin da ya shafi bangaranci kuwa, za mu ga cewa a Kudu-Maso-Yamma, idan ka cire Ondo, Arewa-Maso-Yamma da Arewa-Maso-Gabas, idan ka debe wasu jihohin daga cikinsu, duk sun fada hannun jam’iyyun adawa. A yanzu, an bar wa PDP jihohin yankin Arewa-Ta-Tsakiya, Kudu-Maso-Gabas da kuma Kudu-Maso-Kudu, su ma ba gaba daya ba, domin kuwa dole ne za ta fuskanci kalubale, har ma daga yankin mahaifar Shugaban kasa.
Wannan al’amari yana da kyau da tasiri a siyasance, domin kuwa yana bayyanar da darasi abin koyo, na yadda ya kamata a rika gudanarwa da tafiyar da jam’iyyun siyasa. Idan mun waiwaya baya, abin da ya fara share wa canjin shekar ’yan PDP, shi ne zaben Bamanga Tukur da aka yi a mtsayin Shugaban Jam’iyya, wanda wasu suka rika kokawa da shi, cewa ya faye tsoma baki cikin al’amuran dab a su kamata ba, ga shi da nuna iko, kamar kuma yadda suka ce ba ya da tasiri a siyasance. Al’amarin ya sake rincabewa ne a lokacin da aka tafka badakalar zaben shugabancin kungiyar Gwamnonin Najeriya, inda kungiyar ta dare gida biyu; daya gidan kuma ya kasance yana da goyon bayan Shugaban kasa da na Tukur. daya bangaren kuma, sai aka yi ta yi masa barazanar cewa za a kore shi daga PDP, aka yi ta tsorata shi da jami’an tsaro da sauransu.
Su dai gwamnoni suna da cikakken ’yancin da za su canja sheka, domin kuwa su gwamnojin jihohinsu ne, ba na jam’iyyunsu ba. Kawai abin da za a iya cewa shi ne, bai dace a ce gwamnan da ya ci zabe a wata jam’iyya, ya tsallake ta ya fada wata ba. Ta hakan ma, PDP ba za ta kafa wannan hujja ba, domin kuwa a can baya, ta daure wa wasu gwamnonin gindi, suka baro jam’iyyunsu suka shigo cikinta.
Wata matsala da za ta shafi PDP kuma ita ce, rasa rinjayen membobin da za ta yi a Majalisun Tarayya, domin kuwa mafi yawa daga membobinta sun tsaya cikinta ne kawai saboda kujerun da suke rike da su. PDP na iya kokarin dakile wannan canjin sheka da ’ya’yanta suke yi, amma mu a nan muna ba dashawarar ta bi al’amarin ta hanyoyin da suka dace, domin kauce wa ruruta wutar rigima a siyasar Najeriya.
Idan an zo wajen yakin neman zabe, kamata ya yi a yi shi da dacewa da hikima. Ya dace PDP ta lura da kundin tsarin mulkinta wajen tafiyar da al’amuranta, ta yadda ’ya’yanta za su iya tafiyar da ra’ayinsu, madamar ya dace da kundin. Haka abin ya kamata ya kasance, musamman ma a yayin da muke tunkarar zabubbuka a 2015. Ita kuma jam’iyyar adawa, ya kamata ta ba mara da kunya, ta karyata jita-jitar da ake yi, cewa suna adawa ne kawai domin bukatar kansu, ba ta al’ummarsu ba. Ya dace su nuna kishi ta hanyar kyautata wa al’ummar kasa.