✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun bacewar Naira bilyan 24 na fenshon ’yan sanda

Ga dukkan alamu dai an shiga kakar salwance-salwancen kudeden al’umma a Najeriya, musamman ma dai da a yanzu aka samu sabon batun sulalewar Naira biliyan…

Ga dukkan alamu dai an shiga kakar salwance-salwancen kudeden al’umma a Najeriya, musamman ma dai da a yanzu aka samu sabon batun sulalewar Naira biliyan 24 daga Asusun Fenshon Jami’an ’Yan sanda. A kwanakin baya ne Babbar-Daraktar bangaren Kula Da Tafiyar Al’amuran Fansho (PTAD), Nellie Mayshak ta shaida wa Kwamitin Bin Diddigin Baitulmalin Gwamnati na Majalisar Wakilai Ta Tarayya cewa Naira biliyan 24 da aka ware domin biyan fanshon ’yan sanda a 2010 sun yi batan dabo.
Domin tantance yadda al’amarin yake, kwamitin ya gayyaci Ministar Kudi, Misis Ngozi Okonjo-Iweala da Akanta-Janar Na Tarayya, Jonah Otunla, Odita-Janar Na Tarayya Mista Samuel Ukura da Babban-Darakta Na Ofishin Kasafin Kudi, Bright Okogwu, domin su yi karin bayani. Haka kuma, sun gayyaci bankin First Bank Plc, inda nan Mayshak ta ce aka yi ikirarin an adana kudin, domin su bayar da shaidar ko an taba yin wannan ajiya a bankin  nasu.
Shi kuwa mai binciken kudi na cikin gida a Ofishin Fansho, Adeyemo Julius Adebolu, wanda yana aiki a ofishin lokacin da aka amshi kudin, ya ba da tabbacin cewa babu shakka an amshi adadin kudin a 2010 domin biyan ’yan fansho. Ya kara da cewa, a lokacin har sai da ya ba da shawarar cewa a adana kudin a bankin First Bank Plc. Ya ce tun daga lokacin nan bai kara jin duriyar kudin ba, domin an rufe masa ciki, duk da cewa an dauki hayar wani kamfanin kwararru domin tafiyar da al’amuran kudin, alhali aikin hukumar ne ta tafiyar da al’amuran kudin a hukumance.
A wani jawabi da jami’in hulda da jama’a na Misis Okonjo-Iweala ya bayyana, ya karyata batun cewa kudin sun salwanta. Ya ce abin da ya faru shi ne, Ministar ta shaida wa Kwamitin Majalisar Dattijai mai kula da al’amuran fansho cewa ta bayar da umurni ne cewa lallai a dakatar da asusun domin kare shi daga almundahana.
Idan dai har haka ne an dauki wannan muhimmin mataki, ta yaya kuma za a ce ofishin da ke da alhakin gudanar da kudin bai sani ba kuma ya kasa bayyana haka, har sai da sabuwar shugaba ta zo ofishin, bayan shekaru hudu da faruwar al’amarin? Haka kuma rashin wasu kwararan takardun cudanya game da al’amarin kudin tsakanin ofishin ministar da na Asusun Fanshon ’Yan sanda ya zama abin al’ajabi. Babu shakka ya dace a bincika kuma a tantance abin da ya faru da kudin nan a tsawon shekara hudu da suka gabata.
Sai dai kuma irin yadda ministar ta bayar da amsa kan batun kudin bai saba ba da yadda ake ta samun irin wadannan matsaloli, domin haka ma da aka yi ikirarin Naira biliyan 500 ta Asusun Rarar Mai (Sure-P) sun salwanta, ministar ta ce ba su bace ba. Haka abin yake da aka yi batun batan Dala bilyan 20 na danyen mai, da ba a saka su cikin baitulmalin gwamnati ba. Abin tambaya shi ne, shin wadannan kudade sun salwanta ne, ba a kai ga zuba su a asusu ba ko kuwa dai kawai an sace su ne?
Idan muka koma batun kudaden fansho, har yanzu ba aji batun yadda za a magance matsalolin dubban ’yan fansho ba, wadanda domin a sama musu sauki ne aka bayar da makudan kudin. Idan har an ce an dakatar da asusun da aka ajiye kudin nasu ne, me ya sanya ba a bayyana haka ba tun 2010? Wane mataki aka dauka domin hana sace kudin, kamar yadda Misis Ngozi ta ankarar?
Ana nuna halkin ko-in-kula da hakki ’yan fansho, yadda ake rike kudinsu a ki biya a kan kari. Ga jami’an gwamnatin da suke haka, laifi ne babba, wanda ya kamata duk wanda aka kama da haka a hukunta shi. Irin yadda ake ta zargin cewa kudin fenshon ’yan sanda ya hadu da kuraye, abin takaici ne, kuma hakan yana kara bata sunan Gwamnatin Jonathan ne.
Muna shawartar ’yan majalisa da ke bin kadin batun, da su yi duk abin da za su yi domin tabbatar da cewa an gyara al’amarin. Kada su amince da batun cewa ai komai lafiya lau yake. Ya zama wajibi a gano inda wadannan Naira biliyan 24 suka makale, sannan a ba da su ga masu hakki, kamar yadda aka nufa tun da farko, ba tare da bata lokaci ba. Idan kuwa an gano da wata almundahana a ciki, to a yi gaugawar mika al’amarin ga hukumonin yaki da almundahana domin su yi aikinsu a kai.