Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamntinsa za ta ci gaba da bin diddigin shari’ar zargin aikata batanci da ake yi wa Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara har zuwa lokacin da za a kammala ta.
Ya bayyana matsayin gwamnatin ne lokacin da ya kai ziyarar Sallah ga Halifan Darikar Kadiriyya, Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara a Gidan Qadiriyya da ke Kano ranar Juma’a.
- ’Yan damfara sun dura wa mutum 800 ruwa a matsayin rigakafin COVID-19
- ’Yan sanda sun kama masu luwadi 5 a Kano
Kakakin Gwamnan, Malam Abba Anwar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Juma’a.
Ganduje ya ce, “Muna farin cikin jin cewa muna yin abin da ya kamata a kan lamarin.
“Gwamnatinmu za ta ci gaba da bin diddiginsa har zuwa lokacin da za a kammala,” inji Gwamnan ta bakin sanarwar.
Ganduje ya kuma yaba wa malamin da sauran takwarorinsa bisa irin rawar da suka taka lokacin da aka gudanar da Mukabala da Abduljabbar a Jihar.
“Muna yaba wa irin rawar da kuka taka yayin Mukabalar; abin ban sha’awa ne ganin yadda malamai suka fafata da shi a lokacin.
“Sun nuna matukar zurfin iliminsu na addinin Musulunci,” inji Ganduje.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin taimakawa wajen kammala ginin Cibiyar Musulunci ta Sheikh Nasiru Kabara da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Tun da farko da yake nasa jawabin, Sheikh Qaribullah ya jinjina wa Ganduje kan irin rawar da ya taka wajen kare martabar Annabi Muhammad (S.A.W.).
“Dukkanmu muna yaba wa irin namijin kokarinka a kan haka, Allah ya saka maka da alheri,” inji shi.
Ya kuma gode masa bisa ga ziyarar wacce a yanzu ya mayar da ita ta shekara-shekara.
A ranar Juma’ar makon da ya gabata ne dai Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Sheikh Abduljabbar a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu, bisa zargin aikata batanci da kuma kokarin tunzura jama’a.
Kotun dai ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 28 ga watan Agusta tare da ba da umarnin ci gaba da tsare malamin a gidan gyaran hali zuwa lokacin. (NAN).