Kotun Daukaka Kara ta Jihar Kano ta jingine sauraran kararraki biyu da ke gabanta kan zargin aikata batanci ga Annabi (S.A.W.) zuwa wata ranar da za a ayyana.
Kararrakin sun hada da na wani matashi mai shekara 22, Yahaya Aminu Sharif da aka yanke wa hukuncin kisa a kotun Shari’ar Musulunci da kuma wani mai shakara 13, Umar Faruk da aka yanke wa hukuncin daurin shekara to 10 a kurkuku.
- Shari’ar Batanci: An jibge jami’an tsaro a kotu
- Kar a bude iyakokin Najeriya —Manoma
- Yadda ake dakile matan Arewa a siyasa —Barista Sa’adat
Tun farkon zaman na ranar Alhamis, Lauya mai daukaka kara kan zargin batanci, Kola Alapinni, ya bukaci kotu ta jingine hukuncin da kotun Musuluncin.
Ya ce yana bukatar haka ne saboda kotun Musuuncin ta saba tsari, ta ki ba shi damar kare kai ko sauraren sa, wanda hakan ya saba da kundin tsarin milkin Najeriya.
A nata bangaren, lauya mai gabatar da tuhuma, Aisha Mahud ta bukaci kotun ta tabbatar da hukuncin da Kotun Musuluncin ta yanke, ta kuma yi watsi da bukatar masu daukaka kara.
Alkalin da ke jagorantar karar, Mai Shari’a, Nasiru Saminu ya dage sauraren shari’ar, ya kuma ce za a sanar da bangarorin biyu ranar ci gaba da sauraren ta.