✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batanci: JNI ta kaurace wa mukabala da Abduljabbar

'AbdulJabbar bai cancanci tallatawar da aka yi masa kan wannan rashin mutunci ba'

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta kaurace wa mukabalar da aka shirya gudanarwa da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wanda ake zargi da yin batanci ga Sahabban Manzon Allah (SAW).

JNI ta ce wakilanta ba za su halarci zaman da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tsakanin Abduljabbar da malaman da ke zargin sa ba ne saboda kungiyar ba ta da masaniya game da tsare-tsare ko matakan da gwamnatin Kano ta yi na gudanar da mukabalar.

Sakare-Janar na Kasa na JNI karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, Khalid Abubakar ya jaddada la’antar batancin da Abduljabbar ke wa Magabata na Kwarai.

“Mun yi zaton gwamnati za ta yi shawarwari sosai kan hanyoyin magance wannan matsalar saboda ba Jihar Kano kadai ta shafa ba; abu ne da ya shafi duk Musulmi a duniya da ke yin addini na gaskiya.

“Mutane da gwamnatin jihar sun zuzuta abin fiye da kima har ta kai ga wasu ke ganin batancin Abduljabbar ga Fiyayyen Halitta (SAW) tamkar wani gwarzo.

“Hasali ma Abdul-Jabbar bai cancanci irin tallatawa da kulawa da aka ba shi ba tun lokacin da ya fara wannan rashin mutunci”.