Babban Lauya n Najeriya mai rajin kare hakkin dan Adam Femi Falana (SAN) zai daukaka kara kan hukuncin kisa da wata Kotun Musulunci ta yanke wa wani matashi da ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar Kano.
A ranar Alhamis Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta sanar da mika wa wakilan Falana kundin hukuncin kisa ta hanyar rataya da Babbar Kotun Musuluncin a Jihar ta yanke wa matashin wanda ta samu da laifin cin mutuncin Manzon Allah a wata waka.
“Bangaren Shari’a ya samu takardar wakilan Falana na neman bayanan hukuncin a ranar Talata kuma an mika masa a ranar Laraba”, inji kakakin ma’aikatar, Babajibo Ibrahim.
Ya ce lauyan na so ne ya kalubalanci hukuncin kotun Musuluncin mako guda kafin cikar wa’adin kwana 30 da Kotun ta bayar na daukaka karar kafin zartar da hukuncin da ta yanke.
A ranar 10 ga Agusta ne Kotun Musuluncin ta yanke wa Aminu Yahaya Sherif mai shekara 30 hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun shi da yi batanci ga Manzon Allah (SAW).
Hukuncin kotun ya sa wasu ikirarin kare hakki suka ce ya yi tsauri, yayin da galibin al’ummar Musulmi ke yabawa da cewa hakan shi ne abin da addini ya tanada kuma zai magance katobarar.
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi alkawarin rattaba hannu cikin gaggawa a kan hukuncin kotun da zarar lokaci ya cika, muddin ba a daukaka kara ba, ko kuma da zarar Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin.
Kotun ta ba wa matashin wanda ke tsare a kurkuku wa’adin kwana 30 ya dauka kara ko kuma a zartar masa hukunci.