✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bashir Hadeja: Abokin ‘manya’ da ake zargi da cin amanar ƙasa

Ana zargin Bashir ne da laifin da ya shafi kasa-da-kasa.

Sunan Bashir Hadeja ya yi fice a fadin Nijeriya a ’yan kwanankin nan bayan da jami’an ’yan sanda na musamman suka kama shi bisa zarginsa da cin amanar kasa, zargin da hukuncinsa na kisa ne a dokokin Nijeriya.

Wata takardar umarnin kama Bashir Hadeja da ke dauke da kwana wata 12 ga Agusta, daga Rundunar ’Yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta yi nuni da cewa ana zargin Bashir Hadeja ne da cin amanar kasa da kuma hannu a cikin shirya zanga-zangar ƙuncin rayuwa da aka gunadar a kwanakin baya a kasar nan.

Bayanai sun nuna cewa Bashir Hadeja wanda ya kasance tsohon hadimi ga wani tsohon Gwamna a Arewa, an ga hotunansa tare da wasu manyan mutane ciki har da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila da sauransu.

Aminiya ta bibiyi lamarin Bashir Hadeja kuma ta binciko wasu bayanai cikin har da harkokin kasuwancinsa da kuma alakarsa da manyan ’yan siyaysa da ’yan kasuwa.

Cikakken sunansa shi ne Bashir Muhammad Umar Mai-Shadai Hadeja.

Mahaifinsa tsohon Darakta ne a Kamfanin Wayoyin Lantarki na NOCACO da ke Jihar Kaduna.

An haifi Bashir Hadeja a Layin Ohinoyi, a Unguwar Rimi, Kaduna, kuma a nan ya yi rayuwarsa sai kuma gidansa na kansa a kan titin Kakino da ke Unguwar Rimin.

An kiyasta shekarunsa a yanzu za su kai 47 kuma mahaifansa duka daga Hadeja da ke Jihar Jigawa suke.

Mahaifinsa Umaru Hadeja kamar yadda aka fi kiransa a Unguwar Rimi makusanci ne ga tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido kuma shi ma kusa ne a Jam’iyyar PDP daga Mazabar Dankoli a Karamar Hukumar Hadeja.

Duk da cewa Bashir na amfani da Hadeja a cikin sunayensa mutanen garin Hadeja sun bayyana cewa bai taba zuwa garin na Hadeja ba.

Wani dan garin na Hadeja, Aminuddeen Musa ya ce “Duk da cewa Bashir na amfani da Hadeja a sunansa bai taba zuwa Hadeja ba a duk tsawon rayuwarsa.

“An haife shi ne a Kaduna kuma a can ya yi rayuwarsa.

“Ya yi rayuwarsa a tsakanin Kaduna da Kano da Abuja amma ba Hadeja ba.”

Dalilin da Bashir ya san ‘manyan’ mutane

Aminuddeen ya kara da cewa, “Bashir mutum ne wanda ya yi amanna da kurda-kurda da ’yan buge-buge wajen neman na kansa, don haka ya san manyan mutane da yawa tun yana dan kimanin shekara 30 kuma a yanzu haka ba wani fitaccen mutum a Abuja ko a wata jiha a fadin kasar nan wanda Bashir ba zai iya harka da shi ba.

“Yana da alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsa da manyan mutane a Abuja da sauran manyan birane a jihohi 36 na kasar nan.

“Amma ina ganin wannan ba zai rasa nasaba da harkar kasuwancinsa ba.

“Bashir ya kasance mai harkar kasuwancin ma’adanai ne ciki har da gwal da sauransu a shekaru da dama.

“Ina kyautata zaton hakan ya ba shi damar yin alaka da manyan mutane a kasar nan,” in ji shi.

Alaƙar Bashir Hadeja da manyan ’yan siyasa da masu riƙe da manyan muƙamai aba ce ba boyayyiya ba domin hotunansa da manyan mutane ka iya tabbatar da haka.

Daga cikin manyan da ya yi hotuna da su har da tsohon Shgaban Kasa Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Femi Gbajabiamila da Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara a Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu da ministocin tsaro Alhaji Badaru Abaubakar da Alhaji Bello Matawalle da sauransu.

Alaƙar Matawalle da Bashir Hadeja

Wani ɗan siyasa a Gusau, Jihar Zamfara, Muhammad Ali Gusau wanda ya san Bashir Hadeja ya bayyana shi da makusancin tsohon Gwamnan Jihar Muhammad Bello Matawalle kuma yana daga cikin muhimman mutane kuma makusantan tsohon Gwamnan.

Ya ce “Duk da cewa Bashir Hadeja ba ya da wani mukami a cikin gwamnatin Matawalle, amma yana daga cikin mutanen da suke da kusanci da tsohon Gwamnan a lokacin da yake kan kujerar mulki.

“Hasali ma ‘Ka-fi Gwamna’ ake kiransa a lokacin. Kusacinsa da Gwamna Matawalle ya wuce misali a wancan lokaci.

“Hadeja na daya daga cikin mutanen da ba su da shamaki da Gwamna Matawalle a lokacin yana Gwamna.

“Yana iya sada ka da Gwamna a duk lokacin da bukatar haka ta tasa ko da kuwa ba a ba ka wani lokaci na ganin Gwamnan ba.

“Amma gaskiya, a fahimtarmu alaƙar da ke tsakanin Matawalle da Bashir Hadeja ta kasuwanci ce kawai.

“Duka su biyun suna kasuwancin gwal don haka suna buƙatar junansu.

“Sai dai ban san abin da ya shiga tsakaninsu ba har suka bata. Ban san lokacin da suka bata ba kuma ban san dalilin haka ba,” in ji shi.

Tambayoyin da ke buƙatar amsa kan kama Bashir Hadeja

Kwamared Bala Abdullahi wani fitaccen dan gwagwarmaya da ke Jihar Jigawa ya bayyana shakkunsa dangane da zargin da ake yi wa Bashir Hadeja na cin amanar kasa da kuma shirya zanga-zangar matsin rayuwa a kasar nan kamar yadda ’yan sandan suka bayyyana.

“Ba wai ina cewa Bashir mai gaskiya ba ne, amma fa akwai wasu tambayoyi da ke bukatar amsa kafin a kai ga cewa tabbas Bashir ya aikata abin da ake zarginsa da shi.

“Na fadi haka ne domin a faifan bidiyon da aka nuna Bashir yana bayani a kan wani gwal da ake zargin an shigo da shi ne daga kasar Libiya, tsohon faifai ne wanda aka dauka kimanin shekara biyu da suka wuce kuma gwal din da aka nuna a cikin faifan na bogi ne.

“To me ya sa sai yanzu ake nuna wannan faifan bidiyo?

“Yaya aka yi Hadeja ya tsallake binciken jami’an tsaro a filayen jiragen sama na kasar Libiya da na Nijeriya, domin na samu labarin an kama shi ne a gidansa a Abuja?

“Me ya sa sai yanzu aka kama shi bayan kuma faifan bidiyon an ɗauke shi ne shekara biyu baya?

“Haka kuma ana zarginsa da safarar makamai ina makaman da aka kama shi da su?

“Ana kuma zarginsa da hannu a cikin zanga-zangar da aka yi a makwannin baya a fadin kasar nan; ta yaya mutumin da ke amfanuwa da gwamnati zai shirya mata irin wannan zanga-zanga?

“Ni dai ina ganin ba shakka akwai wasu tambayoyi da dama da suke bukatar zurfin bincike kafin a kai ga tabbatar da cewa ya aikata abin da ake zarginsa kuma har sai Gwamnatin Tarayya ta bi diddigi kuma an warware su sannan ne za a iya gano gaskiyar lamarin zargin da ake yi wa Bashir Hadeja.

“Don haka shawarata ga Gwamnatin Tarayya ita ce a tsananta bincike a kan wannan lamari kuma a ba Bashir dama ya bayyana abin da ya sani game da abin da ake zarginsa.

“Wannan ne zai ba da dama a san gaskiyar abin da ke gudana a tsakaninsa da Minista Matawalle da kuma zargin da ake yi masa.

“Idan kuwa ba haka ba ina ganin ba za a taba gano gaskiyar lamarin ba.

“Wannan wani al’amari ne mai daure kai kuma da ke bukatar zurfafa bincike a kai wanda kuma bai kamata gwamnati ta yi masa rikon sakainar kashi ba.

“Ita harkar ma’adanai tana da alaƙa mai ƙarfi da harkar ’yan bindiga, don haka gwamnati ta naɗa kwamitin bincike domin bincikar wannan lamari don gano gaskiyar abin da ke wakana.

“Ina da tabbacin in har aka ɗora wa mutane kirki nauyin bincikar wannan lamari za a gano gaskiya a samu shawarwarin da ka iya kawo ƙarshen harkokin ta’addacin a kasar nan,” in ji shi.

Hadimin Matawalle ya bara

Da Aminiya ta tuntubi tsohon hadimin Minista a Ma’aikatar Tsaro, Alhai Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya yi watsi da zargin alaka a tsakanin Ministan da Bashir Hadeja.

Sai dai ya tabbatar da alakar kasuwanci a tsakaninsu wadda ita ma ya ce ta wani dan lokaci ce inda daga baya Ministan ya yanke alakar bayan ya fahimci Bashir na zaluntarsa a harkar kasuwancin.

Ya ce “Matawalle da Bashir Hadeja sun yi kasuwanci tare, amma lokacin da Matawalle ya fahimci Bashir na cutarsa sai ya yanke alaƙarsa da shi.

“Duk da cewa ni hadimin Matawalle ne a lokacin yana Gwamna amma a gaskiya ban san Bashir Hadeja ba, kuma ban ma taba ganinsa ba.

“Hasali ma sai bayan da Matawalle ya yanke alaka da Bashir sannan ya zama makiyi ga tsohon Gwamnan.

“A gaskiyar lamari ma Bashir ya yi amfani da alakarsa da manayan mutane ne aka kwace mana nasarar da muka yi a zaben shekarar 2023.

“Mai gidana Matawalle na da makiya da dama a siyasa, hasali ma su ne suke shirya masa wadannan kutungwila domin ganin sun raba tsakaninsa da Shugaba Tinubu.

“Ai Bashir Hadeja ya yi hotuna da manyan mutane ciki har da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Shugaba Tinubu da Femi Gbajabiamila da Nuhu Ribadu, amma duka ba a ambaci sunanyensu ba sai na maigidana Matawalle.

Bashir Hadeja tare da Shugaba Tinubu

“Idan har an samu Hadeja da laifin cin amanar kasa, to, a hunkunta shi kamar yadda dokar kasa ta tanada kuma za mu ci gaba da bin lamarin har karshe don ganin an tabbatar da adalci,” in ji shi.

Dattawan Arewa sun nemi a yi bincike

Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Abdul-Azeez Suleiman ya bayyana takaicinsa a kan kama Bashir Hadeja, inda ya bayyana lamarin “mai daga hankali” da barazana ga zaman lafiyar kasa.

Ya ce abubuwan da aka bankado wadanda suka hada da safarar miyagun makamai da cin amanar kasa laifuffuka ne da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar kasa.

“Duk da cewa ba mu tattauna wannan matsalar a matakin kungiya ba, amma a matsayina na dan kasa ina fadi da karfin gwiwa cewa bayanai kan kama Bashir na da ta da hankali kuma abubuwan da aka ce an gano a lokacin kamun babbar barazana ce ga ’yanci da zaman lafiyar kasar nan.

“Ya kamata gwamnati ta zurfafa bincike a kan lamarin don gano gaskiyar batun da daukar matakan da suka dace,” in ji shi.

Bashir Hadeja na tsare – ’Yan sanda

Sai bayan mako guda da kama Bashir Hadeja, ’yan sanda ba su yi cikakken bayani kan dalili kama shi ba.

Amma binciken da ɗaya daga cikin wakilan Aminiya ya yi ya gano cewa Bashir Hadeja na tsare ne a hedikwatar rusasshen sashen musamman da ke yaki da ’yan fashi da makami (SARS) da ke Abuja.

Wasu jami’an sashen da ba su son a bayyana sunayensu sun tabbatar wa wakilinmu cewa “Tuhumar da ake yi wa Bashir Hadeja lamari ne babba kuma hakan ne ya sa jami’anmu ba sa son yin bayani a kai.”

Wani daga cikin jami’an ya ce “Ana zargin Bashir ne da laifin da ya shafi kasa-da-kasa wanda hakan ke nuni da cewa dole a yi kaffa-kaffa wajen binciken.

“Don haka zai fi kyau mu fara aikinmu kafin duk wani bayani da za a yi wa ’yan kasa.

A lokacin da wakilinmu ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sanda ta Kasa, Olumuyiwa Adejobi ya ce, “Yana tsare.”