An kai fitaccen mawakin yabon Manzon Allah (SAW) Bashir Dandago gaban kotu, bisa zargin neman tayar da zaune tsaye a Jihar Kano.
A halin yanzu an riga an kai mawakin Kotun Majistare da ke unguwar Nomansland, ana jiran isowar lauyan gwamnati don fara shari’ar zargin Bashir Dandago da neman tayar da tayar da tsaye.
- Yadda mutanen Jingir suka yi wa ’yan bindiga kofar rago
- Yadda aka ninka kudin jirgi zuwa Arewa bayan dakatar da Azman
Hukumar Tace Fina-finai da dabi’i ta Jihar Kano ce ta tsare mawakin bisa zargin sa da neman tayar da fitina a Jihar a wata sabuwar wakar da ya fitar wadda a cikinta yake zagin wasu fitattun malaman Islama.
Sugaban Hukumar, Isma’ila Na’abba Afakalla ya ce a cikin wakar da mawakin ya fitar ba bisa ka’ida ba, ya rika goyon bayan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ake zargi da cin zarafin Sahabban Manzon Allah (SAW).