Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) ya ce bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 46.25 a watan Disamban 2022.
A wata sanarwa a ranar Alhamis, DMO ya ce an samu karin sama da Naira tiriliyan bakwai daga abin da kasar ta mallaka a shekarar 2021.
“Jimillar Bashin Jama’a wanda ya kunshi bashin cikin gida da na kasashen waje na Gwamnatin Tarayya da kananan hukumomi daga (Gwamnatin Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya), ya kai Naira Tiriliyan 46.25 ko kuma dala biliyan $103.1, kwatankwacin adadin ranar 31 ga watan Disamba, 2021, na Naira tiriliyan 39.5 wanda ya yi daidai dad ala biliyan $95.77.
“Ta fuskar hada-hadakuwa, jimillar bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan 27.55 daidai da dala biliyan $61.42, yayin da jimillar bashin waje ya kai Naira tiriliyan 18.7t daidai da dala biliyan $41.6.
Ofishin ya bayyana cewa dalilan da suka sa aka kara samun yawan bashin gwamnati; su ne sabbin rancen da Gwamnatin Tarayya da na kananan hukumomi suka yi, na farko, don samar da gibin kasafin kudi da aiwatar da ayyuka.
“Bayar da bayanan lamuni da gwamnati ta yi don daidaita wasu lamura shi ma ya ba da gudunmawa wajen karuwa bashin.”
Sai dai ta ce kokarin da gwamnati ke ci gaba da yi na kara samun kudaden shiga daga albarkatun mai da wadanda ba na mai ba ta hanyar tsare-tsare irin su Dokar Kudi da kuma dabarun tattara kudaden shiga na iya tallafawa dorewar bashi.