✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka Da Sallah Gizagawan Zumunci1

Sallah bikin daya rana, ta wuce ta bar wawa da bashi, kamar yadda Hausawa ke yi mata take. Babu shakka Allah Ya nuna mana Babbar…

Gizagawan Zumunci, jim kadan da kammala taron rantsar da shugabanni, a Zariya, kwanakin baya.Sallah bikin daya rana, ta wuce ta bar wawa da bashi, kamar yadda Hausawa ke yi mata take. Babu shakka Allah Ya nuna mana Babbar Sallah lafiya, domin kuwa a ranar Talatar da ta gabata ne al’ummar Musulmi na fadin duniya suka hau idi. Sai mu ce Allah Ya maimaita mana ta badin-badada lafiya.
A wannan Sallah, muna rokon Allah Ya ba mu mafita daga fitintinu da bala’o’in da suka dade suna addabar al’ummarmu ta Najeriya da ma na duniya baki daya. Muna rokon Allah Ya kawo mana dauki, Ya ba mu ingantattu kuma adalan shugabanni. Allah Ya kawo mana karshen yaje-yajen aikin da suka zame mana alakakai a kasar nan. Amin-summa-amin!
***
Farfesa Yusuf Adamu, 08034064325, daya daga cikin iyayen Gizagawan Zumunci, ya samu tsautsayi, inda ya yi rauni a gwiwarsa, har ma an yi masa aiki kuma yana samun sauki. Da fatan za a sanya shi cikin addu’a. Allah Ya sawwake, Ya sa kaffara ne, amin.
***
Sanarwa: Tawagar Gizagawan Jihar Kano, na farin cikin gayyatar dukkan shugabannin jihohi da dukkan masu rike da madafun iko na kasa da jihohi; gagarumin taron goron Sallah, wanda za a yi a gobe Asabar, a dakin taro na Imamu Wali da ke layi na uku, Unguwar Janbulo; karamar Hukumar Gwale a birnin Kano, da karfe 10 na safe. Domin karin bayani, a tuntubi: 08082438650 ko kuma 08067752671. Allah Ya ba da ikon zuwa amin.

  Sakonnin Sallah Daga Gizagawan Zumunci

Kamar yadda suka saba, zaratan Gizagawa sun aiko da sakonnin gaisuwar Sallah ga daukacin al’umma. Ga abin da suke cewa:
Abubakar Hamisu Yankatsare, 08032634625 (GZG087FTK): “Salam. Gizago, barkanmu da wannan lokaci. Ina taya ka tare da dukkan Musulmin duniya murnar zagayowar Babbar Sallah. Allah (SWT) Ya maimata mana, amin. Malam Gizago, zan yi amfani da wannan dama domin in ja hankalin Gizagawa da mu kyautata zumuntar da ke tsakaninmu. Abin da ya sa na ce haka shi ne, ganin irin raunin da muka samu wajen sadar da zumunci a tsakaninmu, kamar yadda muka saba. Zumuncinmu ya fi ingantuwa a shekarun baya kuma kowa shaida ne cikinmu, domin ba yadda za ka kwashe kwana biyu ko uku ba ka ji kiran wani ya shigo maka ba amma ban da yanzu, koda kuwa mene ne ya faru, sai dai in ka shiga dandalin Facebook, wanda yin haka ba karamin koma baya ba ne ga wannan kungiya. Ai ba kowa ne yake cikin Facebook ba kuma ba kowa ne yake shiga dandalin ba. Ya kamata mu yi gyara, domin inganta zumuntarmu.”
Sanusi Musa CBN, 08038320203 (GZG105BAU), Shugaban Gizagawan Jihar Bauchi ya ce: “Assalamu alaikum. A madadin ni kaina da iyalina da sauran Gizagawan Jihar Bauchi, muna masu farin cikin taya al’ummar Musulmi murnar Babbar Sallah. Allah Ya sa an yi a sa’a kuma Ya sa karbabbiya ce. Daga karshe, ina jan hankalin Gizagawa a kan zumunci, domin babban abu ne ga addinin Musulunci; domin zai iya kai mu ga tsira a ranar gobe kiyama. Allah Ya sa mu dace, amin. Kuma ina yi wa daya daga cikin iyayenmu na Jihar Bauchi Barka Da Sallah, wato Alhaji danlami Babantakko. Da fatan ya yi Sallah lafiya.”
Sani Ibrahim G-Site, 08182898889 (GZG496KTN), yana cewa: “Ina mika sakon taya murnar Sallah ga daukacin Gizagawan Zumunci da sauran al’ummar Musulmi baki daya. Allah Ya maimaita mana, amin.”
M. K. Adam Gombe, 08065432898: “A yayin da muka gabatar da Babbar Sallah lafiya, ina mika sakon Barka Da Sallah gare ka da daukacin Gizagawa da dukkan al’ummar Musulmi. Allah Ya amsa mana ibadojinmu kuma Ya sa albarka da alheri ga sauran kwanukan rayuwarmu. Barka Da Sallah!”
Sunusi Sani Dala, 07057654750: “Salam. Gizago, a mika mani gaisuwar Sallah ga dukkan Musulmi da Gizagawan Zumunci. Gaisuwa ta musamman ga Asiya Nuhu.”
U.S.A Yola, 08035038759: “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! La’ilaha illallah, Allahu Akbar! Wa lillahil hamdu. Takabbalallahu minna wa minkum!”
Kabir Sakaina Malumfashi, 07039769596: “Allahu Akbar! Haza yaumul akbar, yaumul barakat. Alhamdu lillahi ala ni’imatil Islam. Allah Ya yafe mana, Ya yi mana jagora kuma Ya amshi dukkan ibadojinmu. Barka Da Sallah!”
Aliyu danlabaran Zariya, 08036158781: “Sahabban Annabi (SAW), idan sun hadu da juna a rana irin ta yau, sukan ce wa juna: ‘Takabbalallahu minna wa minkum!’ Barkanmu da Sallah!”
Saddik Rishi, 08030460090: “Ina taya ’yan uwa Musulmin duniya murnar Babbar Sallah. Allah Ya sa an yi bukukuwan Sallah lafiya, Allah Ya dawo mana da zaman lafiya a Arewacin Najeriya, Ya kuma ba mu shugabanni nagari a Najeriya. Amin-summa-amin!”
Adamu Usman Katsina, 08169957978 (GZG318KTN): “Ina taya al’ummar Musulmin duniya murnar zagayowar Babbar Sallah. Da fatan Allah madaukakin Sarki Ya karbi ibadojinmu, amin.”
Shi kuma Auwalu Yahya, 08062172919, ta’aliki ya yi kan mukalar da na gabatar a makon jiya, inda ya ce: “Idan aka raba Najeriya, mu Arewa za mu sha wahala saboda rikicin addini tsakanin Musulmi.”
Abdullahi Yakubu, 08091456325 (GZG116NAS): “Salam. Barka Da Sallah ga dukkan Gizagawa. Allah Ya maimaita mana ta badin-badada. Amin.”
***
A wannan makon kuma, ga sababbin Gizagawan da suka dace da rijista:
1-Usman Yunusa Rijiyar Lemo, Kano, 08187666225 (GZG595KNO). 2-Salisu Umar Gusau, 07050205633 (GZG596ZMF). 3-Alhaji Bature Maikilo, Kano, 07061590773 (GZG597KNO). 4-Muhammad Baballe Gambo, Kano, 08132841127 (GZG598KNO). 5-Salisu Garba Udubo, Bauchi, 08030609676 (GZG599BAU). 6-Aminu Ahmad Kazaure, 08022845175 (GZG600JGW). 7-Muhammad Jungudo, 07034924275 (GZG601ADW). 8-Isa Mu’azu Katsina, 08094608663 (GZG602KTN). 9-ASP Adamu Biu, Kwadon, Gombe, 08060302849 (GZG603GMB). 10-Abdullahi Sunusi Jos, 08172929607 (GZG604FLT). 11-Ali kofar Wambai Kano, 08171518726 (GZG605KNO).
Gizago na taya ku murnar shiga tawagar zumuncin Gizagawan Zumunci!