A karshen makon jiya ne kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya fara yunkurin fadada filin wasansa da ke Sifen da ake wa lakabi da Nou Camp.
Kulob din yana yunkurin fadada filin wasansa mai cin ’yan kallo dubu 90 ne zuwa wanda zai dauki kimanin ‘yan kallo dubu 105.
A kan haka ne kulob din ya gudanar da kuri’ar jin ra’ayin magoya bayansa don neman shawararsu kafin a zartar da hukunci.
Idan hakan ta samu, kulob din zai samu karin kudin shigar da ya kai Yuro miliyan 29 kimanin Naira biliyan 62. Sannan an kiyasta kulob din zai kashe akalla Yuro miliyan 600 kwatankwacin Naira biliyan 128 wajen yin kwaskwarimar filin wasan.
Da farko kulob din ya yi tunanin gina sabon filin wasa ne amma saboda wadansu dalilai da suka fi karfinsa ya yanke shawarar yi wa filin wasan nasa kwaskwarima don fadada shi.
Barcelona ta fara yunkurin fadada filin wasanta
A karshen makon jiya ne kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya fara yunkurin fadada filin wasansa da ke Sifen da ake wa lakabi…