✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta amince ta biya tarar Naira biliyan biyu a kan Neymar

Kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya ce ya amince ya biya tarar Yuro miliyan 5 da dubu 5 a kan zargin yin coge…

Kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya ce ya amince ya biya tarar Yuro miliyan 5 da dubu 5 a kan zargin yin coge a kwantaragin da kulob din ya kulla da tsohon dan kwallon Santos Neymar a shekarar 2013.
Shi dai dan kwallon wanda hukumar kwallon kafa ta Sifen ta shigar da kara a kan tuhumarsa tare da mahaifinsa a kan rashin bayyana takamaiman adadin kudin da ya kulla yarjejeniya da kulob din FC Barcelona a lokacin da ya canza sheka zuwa kulob din al’amarin da ta sa ta shigar da kara a kotu don zarginsa da yin coge wajen biyan haraji. Ganin asiri yana neman ya tonu ne ta sa kulob din ya amince ya biya wannan tara don a sasanta a wajen kotu.
A baya Barcelona ta nuna ta kashe Yuro miliyan 57 ne wajen cefano ’dan kwallon inda ta nuna ta ba tsohon kulob dinsa Santos Yuro miliyan 17 daga cikin kudin da sauran kuma ta biya dan kwallon da iyalansa.
Sai dai rahotanni sun nuna cinikin da dan&nbsp