Barbados ta samu ’yancin kai daga Ingila inda Dame Sandra Mason ta maye gurbin sauraniya Elizabeth a matsayin sabuwar shugabar kasa.
Barbados a ranar Talata, 30 ga watan Nuwambar 2021, ta zama sabuwar kasa da ta samu ’yancin kai a duniya.
- Yadda matan Hausawa suka yi watsi da al’adun al’ummarsu
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutun 15 a Jigawa
An rantsar da, Dame Sandra Mason a matsayin sabuwar shugabar kasa a bikin da aka gudanar a Bridgetown, babban birnin kasar.
BBC ya ruwaito cewa, Yariman Wales da kuma mawakiya Rihanna ’yar asalin kasar sun halarci bikin.

Hoto: Getty Images
A cikin jawabinsa Yarima Charles ya amsa abin da ya kira ayyukan cin zali na ɓautarwa da ƙasar da ke tsibirin Caribbean ta fuskanta.
Yanzu Barbados ta kawo karshen karfin ikon Birtaniya, wanda ya hada da sama da shekaru 200 na kasar ta kasance mashigin fataucin bayi.

Hoto: Getty Images
Sarauniyar Ingila ta aika da fatan alheri da farin ciki da zaman lafiya mai dorewa ga makomar kasar, tare da cewa kasar, “tana da tasiri a zuciyarta.”